Da muna sana’ar mune don lalata tarbiyya da a yanzu zaman lafiya ya gagari uban kowa a Nageriya, cewar Ado gwanja

Shafin punch hausa ya wallafa wani labari na shirar da sukayi da jarumi kuma mawaki Ado gwanja, a cikin shirar da sukayi Ado hwanja ya fadi wasu abubuwan wanda jama’a sukayi ta cece-kuce a kai.

Sai dai kuma wannan wallafa da shafin punch hausa sukayi kan abin da Ado gwanja ya wallafa ya janyo maharawa, inda wasu mutanen suke ganin batun da Ado gwanja yayi akwai kamshin gaskiya a ciki, wasu kuma suke ganin bai dace fadi wannan magana ba kuma kawai soki burutsu ne irin nasa.

Inda jarumi Ado gwanja yake fadin cewa, sakommu yana ishewa fiye dana malamai, ana yarda damu kuma ana kallon mu kuma ana sauraranmu fiye da yadda akewa malamai, sabida a halin yanzu mutane sunfi karkata ga harkar nishadi fiye da jin wa’azi, sabida haka mafita kawai shine a daina kyamatar harkar malamai sushigo ciki domin a musulintar da harkar yadda zata dace da addini da kuma al’adar mu.

Haka ilimin boko malamammu na wancan lokacin da kuma mutanen kirki suka ginda kyamatarshi akabar harkar a matsayin kafirci, sai ya zamana mafi yawan wadanda suke da ilimin a wancan lokacin basu da ilimin addini sai gashi a yanzu su suke mulkar al’umma.

Sannnan kuma jarumi Ado gwanda ya sake wata wallafa wanda jama’a sukayi ta cece-kuce har ma da masu muhawara a kai, inda yake cewa.

Da muna sana’ar mune don lalata tarbiyya da yanzu zaman lafiya ya gagari uban kowa a Nageriya, kaso biyu cikin uku na al’umma suna bibiyarmu kuma suna gamsuwa da duk wani abu da mukeyi to wannan tasa muke taka tsantsan da wajan yin fina-finai da wakokin da muke.

Saudayawa zakaga mutum har kuka yake yayin daya kalli wani fim mai ban tausayi ko kuma kaga mutum yana jin haushin actor na fim kawai sabida roll din da akasa acoton zakaga roll ne na mugunta iya wannan zaisa a gane irin imanin da mutane sukai mana, a cewar jarumi kuma mawaki Ado gwanja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button