Ina bukatar a taimakamin wajan ganin nafi kowacce jaruma daukaka a kannywood, cewar jaruma Nuwaira Abdullahi

Kamar yadda kuka sani a masana’antar shirya fina-finai ta kannywood ana yawan samin sabbin jarumai da suke shiga masana’antar, sannan burin jaruman shine suyi suna yadda duniya zata sansu.
Ana haka sai wata sabuwar jaruma mai suna Nuwaira Abdullahi ta bayyana wanda kuma ita ‘yar asalin garin jos ce sannan kuma bata jima da shiga masana’antar ta kannywood ba, amma itama da Alamu babban burinta shine ta sami dama yadda zatayi fice a masana’antar ta kannywood.
Jarumar wacce ta fara fitowa a cikin shirin fim din Kona gari wanda aka shirya shi a shekarar 2020, sannan kuma jarumar ta bada gudun mawa sosai a cikin shirin wajan nuna kokarinta, inda jama’a suke ganin idan jarumar ta sami dama nan gaba kadan to tabbas burinta zai iya ciki.
A lokacin da jaruma Nuwaira Abdullahi suka tattauna da wakilin jaridar Damukaradiyya, jarumar ta bayyana dalilin ta na shiga harkar ta fina-finai.
Inda jarumar ta bayyana cewa, ina son duniya na sanni nayi fice a cikin harkar fim, don haka inada burin na sha gaban kowacce jaruma a cikin masana’antar ta fina-finai ta kannywood, domin suma mata ne kamar ni don haka inda karfin gwiwar da zan taka duk wani matakin da duk wata mace zata taka don tayi fice a duniya.
Jarumar ta kara da cewa, nasan daukaka ta Allah ce kuma shi yake bayarwa, don haka inada kyakkyawan fata nima Allah zai bani daukakar dazan cimma burina, jarumar tace ina bukatar naga na sha gaban kowacce jaruma a masana’antar ta kannywood.
A karshe jaruma Nuwaira Abdullahi tayi fatan alkairi ga duk wanda ya taimaka mata, don ganin ta cimma burinta na ganin ta sha gaban kowacce jaruma a masana’antar ta kannywood.