Ma aikatan lafiya da a kakama da karkatarda katan din gidan sauro dari da Tara 109 A Jahar Gombe

Ma’aikatar Lafiyar Jihar Gombe, ta sanar da kama Ma’aikata 7 wanda suke aiki a hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Gombe wanda reshen Kanana hukumomin Kwami da kuma Billiri, bisa zargin su da karkatar da Katan 109 na gidan Sauro wanda za’a raba a Jihar Gomban Wanda Hukumar lafiya tabayar Domin Al ummar Jahar ta Jahar Gombe.

Da yake Jawabi ga manema Labarai Daya daga Cikin manema labaranmu yasum nasar Nado Dukkanin bayanan wanda.

Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya na Jihar Dr Habu Dahiru, ya ce kimanin Katan 100 wanda aka bada na gidan Sauro daga karamar hukumar Kwami ne suka bata, kuma tuni suka kama mutane 4 bisa zargin su da sahannun su a karkatar da kayan.

Kwamishinan ya ce sauran Katan 9 na gidan Sauron sun bata ne a karamar hukumar Billiri kuma tuni suka kama wasu daga Cikin Ma’aikata Lafiya 3 bisa zargin su da hannusu a batan kayan da a kakawo na gidan sauran.

Dr Dahiru, ya ce daga bayanan sirrin da suke samu ya yi nuni da cewa an kama motocin da suka yi safarar gidan Sauron zuwa wasu wurare na daban Wanda direbobin motar suka bayyana Wanda suka sasu safarar.

Kazalika, ya ce yawan Adadin gidan Sauran ya kai dubu 5,450 wanda aka karkatar da su inji direban da yayi safarar kayan.

Kwamishinan ya ce matukar aka kama mutanen da laifin, za’a hukunta su kamar yadda kundin hukunta Ma’aikatan Gwamnati ya tanadar.

Kukasance tare damu akan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button