Noor diyar shugaba Muhammad Buhari ta bayyana gaskiyar labari game da cewa dan talakawa zata aura

Kamar yadda kuka sani a kwanakin baya da suka gabata, gabannin auren dan shugaban kasa Yousuf Buhari, an sami wani labari da Noor Muhammad Buhari ta wallaf wanda ya dauki hankulan jama’a da dama.

Inda Noor Muhammad buhari ta wallafa cewa, ni dan talaka zan aura domin nuna halacci ga talakawan Nageriya da suka soyayyar su ga babana.

Noor Muhammad Buhari ta kasance ita kadai ce wanda ta rage a cikin ‘yayan shugaba Muhammad Buhari wanda batayi aure ba, amma sai ta bayyana cewa ita dan talaka zata aure domin ta nuna halaccinta ga talakawan Nageriya da suka nunawa mahaifinta soyayya.

Sai kuma a wannan lokacin muka sami wani saban labari na Noor Muhammad Buhari inda tace, duk wanda yake tambaya a kanta a shafinta na sada zumunta na instagram, inda har wasu suka fara yi mata tambaya da cewa wai hin da gaske ne tace dan talakawa zata aure.

Inda Noor Muhammad Buhari ta bada amsar a cikin wani hoton ta data wallafa kamar yadda zaku gani a cikin hoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button