Gwamnan Alfawa malam Adamu na shirin kwana casa’in ya zamo gwarzon jarumi a shekarar 2021

Shahararran jarumi kuma jajircacce wanda yayi fice a shirin fim din Kwana casa’in 90 wanda Arewa24 take harkawa a duk mako, Ahmad gidan dabino M.O.N, wanda jama’a suka fi sanin sa da Malam Adamu gwamnan Alfawa.
Ya maza gwarzon jarumi a shekara ta 2021 a taron da aka gudanar na fidda gwarzon jarumi A Africa, a wannan Award da akayi na shekarar 2021 a jamhuriyar Nijar.
Kamar yadda jaridar Damukaradiyya ta tattaro labarin: An gudanar da taron a daren ranar asabar a palais dec cogres niamey, wanda taron ya sami halartar jarumai da yawa daga kasashe daban-daban a Africa.
Malam Adamu ya sami wannan daukakar ne kokarin sa a cikin shirin Kwana casa’in, wanda ta dalilin haka yayi nasara a kan dukkun wasu jarumai da suka shiga gasar da shi, wanda ya sami sa’ar zama shahararran jarumi kuma ficacce a shekarar 2021.
Sannan ba wannan lokacin kadai jarumin ya saba zama gwarzo a cikin jarumai ba, sabida a shekarun baya da suka wuce ya taba yin nasara a gasar daya lashe ta shirin fim din juyin sarauta.