Mun hana haska fina-finan da ake kwacen wayoyi da garkuwa da mutane domin hadarine ga al’umma, inji Afakallah

Kukumar tace fina-finai ta jihar Kano wanda ita take da alhakin tantance duk wani shirin fim da ake gudanarwa, domin gudun matsala kar ana shirin da bai dace ba.
Sannan kuma hukumar ta haranta haska duk wasu fina-finai da ake yin garkuwa da mutane, haka kuma ta haramta haska duk wani fim da ake sayar da kwayoyi da yadda ake shan kwayoyin maye.
Shugaban hukumar tace fina-finan Alhaji Isma’ila na Abba afakallah, shine ya sanar da hakan a wata zantawa da yayi da Freedom Radio.
Afakallah ya cigaba da cewa, duk wani fim wanda ake nuna kwacen waya a hannun Namiji ko Mace, ko ake nuna wata mummunar dabi’a shima bazamu amince a haska shi ba.
Haka kuma shugaban hukumar Afakallah ya bukaci ‘yan jarida dasu taimakawa hukumar wajan wayar da kan al’umma, domin dakile irin wadannan matsalolin sabida hakan zai iya gurbata tarbiyyar matasa da kuma cigaban rayuwar su.
Afakallah ya bayyana hakan ne domin irin wadannan fina-finan na masu garkuwa da mutane, yana taimakawa wajan kara yin garkuwa da mutane wanda hakan ya kasance abune mai matukar hadari a tsakanin al’umma.