Na sha wahala da kalubalen jama’a a rayuwata kamin na sami daukaka a shirin fim na kannywood, cewar jaruma Masa’uda ‘yar agadaz

Kamar yadda kuka sani a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood yawancin jarumai maza da mata, sukan bayyana abubuwan da suke sha musu gaba a rayuwa.
Sai kuma a wannan lokacin jaruma masu’uda Ibrashim wanda aka saninta da ‘yar agabaz, wanda da yawa daga cikin al’umma masu kallon shirin fina-finai basu santa ba, jarumar wacce tayi sharafi a cikin shirin Dadin kowa ta bayyana irin wahalar data sha kamin ta zamo ficacciyar jaruma a masana’antar.
Jaruma masa’uda ‘yar agadaz ta bayyana hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin jaridar Damukaradiyya.
Jarumar ta fara da cewa, to gaskiya na sha wahala kuma na gamu da kalubale da dama a cikin harkar fim, musamman sai kaga wani ya bayyana maka a fili cewa yana sanka sai ka tagi kuma ya zage ka, to irin wadannan na fuskance su da dama sai dai ina yi musu fata na alkairi sabida yanzu komai ya wuce a wajena, sabida idan nace zan lissafa abubuwan suna da yawa.
Sannan kuma an tambayi jarumar dan gane da maganar auren ta, sai ta fara da cewa.
Ni dai a gare ni zabin Allah nake nema duk wanda Allah ya zabamin shi zan aura, don haka duk masu mana kallon muna da buri to mu ba haka muke ba domin shi alziki na Allah ne, don haka ba sai lallai mai kudi zan aura ba miji nagari nake fatan samu.
Wannan shine bayanin da jaruma masa’uda ‘yar agadaz ta bayyana a lokacin da suke tattaunawa da wakilin jaridar Damukaradiyya.