Tirkashi Ankama Wani Mai shekar 50 Da laifin Kaiwa Yan Bindiga Man Fetur A Jahar Katsina

Rundunar Yan sandan Jihar Katsina ta bayyana cewa tayi nasarar kama mutane 5 bisa zargin su da aikata laifukan kaiwa yan bindiga Fetur da kuma Abinci, tare da kama wani mai Garkuwa da mutane.

Kakakin rundunar SP Gambo Isah, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Katsina.

A cewarsa, a ranar 18 ga watan Satumba ne suka samu wata masaniya, wanda ta basu damar kama wani mutum mai shekaru 32 Dan kasar Nijar wanda yake kaiwa yan bindigar Fetur.

Haka kuma ya ce sun kama wani mai shekaru 28 wanda yake zaune a Magamar Jibia, wanda shima yake kaiwa yan bindigar Fetur.

SP Gambo Isah, ya ce rundunar ta yi nasarar kama wani mai shekaru 50 wanda yake zaune a kyauyen Daddara na karamar hukumar Jibia, shima da laifin kaiwa yan bindigar Fetur.

Mai Magana da yawun rundunar ya ce sun yi nasarar kama wani mai shekaru 57 wanda yake zaune a Kofar Guga, bisa zargin sa da laifin kaiwa yan bindigar Fetur.

Kazalika, ya ce mutanen sun amince da laifukan da ake zargin su da shi na kaiwa yan bindigar Fetur a Daji.

To JAMA’A saku it’s ajiyemana ra ayoyinku a comment section Domin Jin tabakinku.

Kukasnce da Dalatopnews ako dayaushe Domin samin shiryeshiryanmu masu kayatarwa don’t forget to subscribe this site.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button