An kama wani gurgu mai suna Haruna buhari wanda yayi barazanar zaiyi garkuwa da makwabcibsa idan bai biya naira miliyan 2 ba

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kama wani gurgu mai shekaru 22, ana zargin gurgun da yin garkuwa da makwafcinsa ina yace a bashi naira miliyan 2 ko kuma ya sace shi.
Matashin gurgun mai suna Haruna buhari ya amsa laifin daya aikata inda yake cewa, a duba nakasar da yake da ita ayi masa rangwame kan laufin da yayi kuma yayi nadama.
Gurgun matashin mai shekaru 22 yana zaube ne a karamar hukumar kankia dake jihar Katsina, inda ‘yan sandan jihar sukayi ram da gurgun kan laifin daya aikata.
Ana zargin gurgun dayin barazana da cewa zai sace wani mutumi idan ba’a biya shi naira miliyan 2 ba, kamar yadda LIB suka ruwauto.
A lokacun da aka damke matashin gurgun tare da nunawa manema labarai shi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Gambo Isah ya bayyana cewa, an kama gurgun Haruna buhari a yayin da yake karbar kudin fansa sannan kuma yayi basaja a wurin da akayi za’a karbi kudin.
SP Gambo Isah ya kara da cewa, bayan kama gurgun da akayi Haruna buhari an tabbatar da cewa, hatta wadanda ba’a tsammanin zasu aikata laifin suma a yanzu suna amfani da wannan damar wajan satar jama’a.
Bayan da aka kama Haruna buhari manema labarai sunji ta bakinsa, amma Haruna bai musanta laifin daya aikata ba, ya bayyana cewa ya kira mutumin wanda makwabcinsa ne yayi masa barazana da cewa in har bai biya kudi naira niliyan 2 ba to zai yi garkuwa da shi.
Haruna buhari yace, yayi nadamar abin daya aikata duk dama shi din mai nakasa ne, amma yana neman yafiya kuma yaba rokon ‘yan sandan suyi masa rangwame kan laifin nasa, kamar yadda LIB ta ruwaito.