Bayan luguden wutar da ‘yan bindiga suke sha a wajan sojojin Zamfara da Katsina sun fara shiga jigar Kano

Haruna Isah Dederi dan majalistar wakilai wanda yake wakiltar mazabar Rogo da karaye, ya bayyana kokensa game da yadda ‘yan suke shiga jigar Kano.
Kamar yadda bayyana cewa, ‘yan bindigar da suke gudowa daga luguden wutar da rundunar sojojin Zamfara da Katsina suke musu, sun fara kaiwa hari karamar hukumar Rogo.
Sannan kuma majalistar wakilai tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin dakile yawon da ‘yan bindiga suke daga wani wuri zuwa wani wurin.
Dan majalistar wakilai wanda yake wakiltar mazabar Rogo, Karaye dake jihar Kano, haka kuma Haruna Isah Dederi ya kara da cewa, sabida luguden wutar da sokoji suke kan ‘yan bindiga a Zamfara da Katsina sun fara tserewa suna shiga jihar Kamo.
A wani kudurinsa daya gabatar a yayin zaman majalista a ranar Talata, ya bayyana cewa a ‘yan makonni da suka gabata maharan sun kai sun kai hari kan wasu kauyuka a karamar hukumar ta Rogo.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito cewa, kauyukan da hate haren ya shafesu sun hada da, Jajaye, Zarewa, Ruwan Bago, Bari, Falgoro, DutsenBan.
A jawabin da dan majalistar yayi ta fadi cewa, idan ba’a dauki matakin gaggawa ba wajan dakile ayyukan wadannan ‘yan bindigar a karamar hukumar Rogo da sauran yankunan dake suke karshen iyakar jigar Kano ba, to maharan zasu bazu zuwa sauran yankunan kuma hakan barazana ne ga zaman lafiyar jihar ta Kamo.
Bayan sauraran wannan kudurin nasa majalistar wakilai tayi kira ga gwamnatin tarayya data ankare game da nasarar da sojojin ke samu a Zamfara da Katsina wanda suke hawowa, ta hanyar daukar mataka a sauran jahohin da abin ya shafa domkin a dakatar da sauya wajan ‘yan bindigar daga wani wurin zuwa wani wurin.