Hauwa ‘Yar Fulanin Gombe ta bayyana dalilin da yasa ta fara harkar waka da kuma kalubalen data fuskanta a rayuwa

Mawakiya Hauwa ‘yar funalin gombe wanda take rera wakokin hausa da kuma na fulatanci, ta bayyanawa duniya makasudin da yasa ta fara harkar waka.

Shahararriyar mawakiyar ta bayyana hakane a wata shira ta musamman da tayi da shafin sadarwa na W TV, inda mawakiyar ta bayyana dalilin da yasa ta fara harkar rera wakokin.

Mawakiyar ta fara da cewa: ni dai sunana Hauwa ‘Yar Fulanin Gombe, nayi primary school da kuma secondary school a garin gombe, kana tace naso na cigaba da karatuna anma Allah bai nufa ba ko sai a nan gaba.

Sannan kuma mawakiyar Hauwa ‘Yar Fulanin Gombe ta bayyana da yasa ta fara harkar waka, inda take cewa.

Lokacin ina secondary school ban gama ba sai nayi aure, bayan auren nawa ya mutu sai na dawo gida na koma makaranta na karasa SSCE bayan na gama na koma gida na zauna, na nemi makaramtu daban-daban amma Allah bai nufa ba sai na fara sana’ar zannuwa na mata, to kasan sana’ar mu ta yanzu bashi yayi yawa kuma abin akwai wahala sai na daina.

Ta kara da cewa: Babban dalilin da yasa na fara harkar waka shine lokacin da kanina ya zama soja sai naji ina bukatar ayi masa waka, sannan kuma ina san macece wanda zata yi masa wakar kamar ni sabida tun farko na taso ne ina sha’awar yin waka, to sai Allah ya kawo kaddara na rasa wacce zata yi masa wakar sabida a lokacin gaskiya mawaka mata.

A lokacin sai nayiwa wani mawaki magana nace ina son ayi min waka ne amma mace nake bukata na rare wakar, sai yace min gaskiya baza’a sami macen da zata yi ba sabida a lokacin babu mawaka mata a garin Gombe, sai ya fadamin cewa to ke kiyi mana sai nace masa ai ni baza iya ba, sai ya kara cemin zaki iya ai zan rubuta miki ne daya rubutamin sai ya bani yace kije kibi yadda na rubuta, dana koma gida bayan kwana biyu muka koma studio da yake a lokacin a cikin garin Gombe studio daya ne, sai munje sai ace sai gobe sannan akwai ranar da sai da shiga cikin wurin da ake rera wakar aka ce nafito sabida zan wahalar dasu tunda wannan lokacin shine farkon fara wakata.

Sai na fito daga cikin wurin shi kuma ya shiga ya gama wakar sa ya fito, sai na shiga tunda na fara rera wakar ban tsaya ba sai da na gama a lokacin sai da kowa ya cika da mamaki a studio din sai kuma kowa ya fara din dadi, sannan mutane suka fara cewa kaji murya kamar ta fantimoti gaskiya kinyi kokari, daga wannan lokacin mai studio din yace zasu karbi lambar waya na idan ana bukatar amshi zasu kirani wannan shine dalilin da yasa na fara harkar waka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button