Advertisement

Jam’iyyar PDP tana zargin gwamnatin shugaba buhari da kare masu daukar nauyin ‘yan ta’addan Nageriya

Jam’iyyar adawa ta PDP tana zargin gwamnatin shugaban kasa Muhammad buhari da kokarin bada kariya ga masu daukar nauyin ta’addanci a Nageriya.

Jam’iyyar PDP ta bayyana kanan ne a yayin martani kan kalaman fadar shugaban kasa cewa FG bazata fallasa sunayen masu nauyin ba, amma zata mai da hankali wajan hukunta su.

Kakakin jam’iyyar PDP na kasa mai suna, Kola Ologbondiyan ya fadi cewa, matakin da FG ya bayyana karara cewa mutanen suna da alaka da jam’iyyar APC.

Jam’iyyar ta PDP ta bayyana hakane a yayin da take game da kalaman kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, cewa gwamnatin tarayya bata da ra’ayi na fallasa ko kuma kunyata masu daukar nauyin ‘yan ta’addan.

FG: Da yake shira da kafar yada labarai da channel TV Femi Adesina yace maimakon fallasa sunayen, gwamnatin tarayya zata mai da hankalinta wajan gurfanar dasu domin a musu hukunci.

Hakan yazo ne bayan da hadaddiyar daular Larabawa, UEA, ta kasa ‘yan Nageriya gida shiga a gerin ‘yan ta’adda.

Kolo Ologbondiyan kakakin jam’iyyar PDP a lokacin da yake mai da martani yace, gwamnatin shugaab buhari ta gaza kawo karshen ta’addanci a fadin kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button