Munyi nadamar yaki da tsohon shugaban kasa Jonathan domin Buhari ya kunyata miliyoyin al’ummar Nageriya, Dattawan Arewa

Shugaban kasar Nageriya Muhammad buhari ya kunyata miliyoyin al’ummar dake Nageriya ciki kuwa har da ‘yan a mutu wanda suke bin jam’iyyar ta APC.

Kakakin dattawan Arewa ya bayyana cewa, sun nadama wajan kawar da Goodlock Ebele Jonathan a shekarar 2015, sannan kuma yayi ka al’umma da su san wanda zasu zaba a shekarar 2023.

Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa, tayi nadama kwarai wajan yaki da tsohon shugaban kasar Nageriya Goodlock Ebele Jonathan, don shigaba Muhammad buhari yaci zabe a shekarar ta 20215.

Kungiyar ta dattawan Arewa tayi Allah wadai da yadda shugaba Muhammad buhari ya kunyata miliyoyin al’umma a Nageriya, ciki har da ‘yan jam’iyyarsa ta Alla Progressives Congress wanda suka taimaka wajan yin aiki tukuru domin yaci zabe.

Kungiyar ta dattawan Arewa ta kara da cewa, shugaban kasar da za’ayi a nan gaba ana so ya kasance zai bi tafarki ba irin na shugaba Muhammad buhari ba.

Kakakin kungiyar ta dattawan Arewa, Dr Hakeem Baba Ahmed, yayi wannan jawabin ne a shirar da yayi da ‘yan jarida a cikin shirin the Morning show na tashar Arise TV a ranar talata.

Ya kara da cewa,  shin akwai wani dan kasar Nageriya wanda shugaba Muhammad buhari bai bashi kunya ba a yanzu, shin akwai wanda zai ce shugaba Muhammad buhari bai gaza ba, munyi masa kyakkyawan zato sannan kuma mun sanar da jama’a cewa suyi watsi da Goodlock Ebele Jonathan, ku zabi Muhammad buhari domin zai yi yaki da cin hanci da rashawa, sannan zai magance matsalar tsaro, zai gyara tattalin arziki, amma ku kalli yanda muke a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button