‘Yan Sandan Jahar Katsina Sun Sami Nasarar Kama Wani Dan Kasar Nijer Da Tallafawa ‘Yan Boko Haram

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta cafke wani mutum mai suna Lawal Shu’aibu, dan shekara 32, dan Maradi a Jamhuriyar Nijar da wasu mutane 4 da ake zargi da sayar da man fetur ga ‘yan bindiga da ke dazukan jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a Katsina, Gambo Isah, ya shaida wa manema labaranmu cewa an kama mutumin a ranar Asabar yayin da yake jigilar man cikin mota kirar Volkswagen Passat.

‘Yan sandan sun ce sauran mutane hudun da aka kama sune Sani Lawal, mai shekaru 28, na Magamar Jibia a Karamar Hukumar Jibia wanda yake kai mai shima a mota kirar Volkswagen Passat, da Abdulrashid Garba, dan shekara 50, na kauyen Daddara a karamar hukumar ta Jibia, wanda yake kai mai a cikin motarsa kirar Volkswagen Golf 3.

Kazalika, a ranar Asabar, an kama wani da ake zargi da samar da mai ga ‘yan ta’adda a cikin dajin, mai suna Shafi’u Haruna, dan shekara 25, na kauyen Anguwan Nakaba da ke karamar Hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina.

To jama’a kina karanto wannan Labaran kaitsaye Da shafinmu Na Dalatopnews Kada kumanta Kudannan Mana alamar kararrawar sanarwa Domin Jin kararrawar shiryeshiryanmu a ko da yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button