Zan Daina Harkar Film idan Na Samu Mijin Aure Cewar Zee Preety Jarumar Kannywood

A Wata Doguwar Hira Da Mujallar Film Tayi Da Jaruma Zulaihat Ibraheem Wanda Akafi Sani Da Zee Preety A Masana’antar Kannywood Ta Bayyana Dalilin Shigowarta Harkar Film Da Kuma Kudurinta.

Jarumar Tace Dalilin Shigowata Harkar Film Shine Akwai Wani Sako Danake So Na Fadawa Jama’a Kuma Alhamdulillah Nasan Sakon Ya Isa Inda Nake So Yaje.

Baya Da Haka An Tambayi Jarumar Wacce Shawara Zaki Bawa Yam Mata Masu Shirin Shigowa Harkar Film?

Jarumar Ta Kada Baki Tace A Gaskiya Harkar Film, Harka Ce Wanda Take Bukatar Ta Kame Kanta Domin Ita Rayuwa Tana Iya Sauyawa A Ko Ina Sannan Kuma Ba Lallai ne Ace Duk Wanda Kuka Hadu Dashi Mutumin Kirki Bane.

Hakan Bayana Nuna Yawanchi Mazan Kannywood Din Bana Kirki Bane Sai dai Baza’a Rasa Balagurbi ba.

Sanna Ta Kara Dacewa Wasu Yam Matan Suna Shiga Harkar Film Ne Domin Suyi Suna A Duniya, Toh Ba Haka Lamarin Yake Ba Daukaka Tana Zuwane Daga Allah Ba Daga Mutum Ba Amma Idan Kika Zamto Mai Kamun Kai Za’a Sanki A ko Ina Har Wajen Dabakiyi Zato Ba.

Daga Karshe An Tambayi Jarumar Ya Maganar Aure Sai Jarumar Ta Kada Baki Tace, Shi Aure Lokaci Ne Kuma Nufi Ne Na Allah Idan Allah Ya Nufa Za’ayi To Za’ayi Kuma Ko Yanzu Na Samu Mijin Aure In Har Muka Dai-daita Dashi Zan Bar Harkar Film Nayi Aure Domin Shi Aure Shine Kan Gaba A Komai Musamman Ga ‘Ya Mace.

Baya Da Haka Mahaifanmu Ma Suna Bukatar Miyi Auren Tunda Ta Haka Aka Samemu.

Ga Wata Videon Da Zaku Kalla Datayi Bayani Cikakke Akan Lamari:

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku Akan Wannan Bayani Na Jarumar Nan Wato Zee Preety Mungode Da Sauraran Wannan Shirin Idan Wannan Shine Karonka Na Farko A Wannan Shafi Munaso Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe, idan Kuma Kun Danna Munaso Kuna Watsa Labaranmu Zuwa Kafafen Sada Zumunta Domin Sauran Jama’a Su Amfana Mun gode!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button