An Jefa wani Jariri A Sokawe Na Bandaki A Cikin Garin Hadejia Jihar Jigawa

Hukumar tsaron fararen hula Civil Defence ta gano wani jariri da aka jefar a cikin sokawe na bandaki a unguwar Kwarin Manu da ke karamar hukumar Hadejia.
Daya Dagacikin Jami’anmu dake Jahar jigawa mazaunin hadejia ya baiyanamana wannan rohotan a yau alkamis 23-9-2021 Da misalin karfe 5:30 Na yamma.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar a jiha, Adamu Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a birnin Dutse.
Ya ce lamarin ya faru ne a jiya bayan Umar Muhammad mai shekaru 47 ya kai rahoto ga hukumar cewa ya hangi wani abu a bandakinsa.
Adamu Shehu ya ce, jami’an Civil Defence garzaya wajen da lamarin ya faru kuma an gano gawar jariri daure a jikin rigar matashin kai a cikin sokawe na bandakin.
Adamu Shehu ya ce, Umar Muhammad yana hannun hukumar ta civil defense wacce ta tsare shi don yi masa tambayoyi.
Ya ce an dauke gawar kuma an kai ta Babban Asibitin Hadejia inda aka tabbatar da mutuwar jaririn.
Kukasnce tare Dani A.Usman Ahmad Domin samin labaran Duniya Kai tsaye.
KU KARANTA WANNAN:
Gwamnatin Barno Zata Hada Kai Da FG Wajan Amfani Da Mika Wuyan Yan Boko Haram
Hukumar (NDLEA) Ta Samu Nasarar Kama Wani Dillalin miyagun kwayoyi A Tashar Jirgin Sama
Duk Iskanchinki Ummi Rahab Ki Kalli Rayuwar Maryam Yahaya Sannan Ki Dauki Darasi
Zuwa makkuna Biyu Aka Dage Taron Jam’iyyar A P C Maimulki Na Babban Taron Jihohi
Tirkashi Ansaki Bidiyon Ummi Rahab Wanda Ta Tonawa Adam A Zango Asiri
An kama wasu mutane su 3 a jihar Kano da laifin fashi da makami na kwacen waya tare da kashe wani
To jama’a zamu iya Jin ra’ayoyinku a sahinmu na comment section Na wannan gidan jaridar na Dalatopnews kada kumanta kudanna alamar kararrawar sanarwa Domin samin sabbin labaran Duniya.