An Yi Nasarar Ragargazar ‘Yan Boko Haram Da ‘Yan Bin Diga Acewar AGF Kuma ministan Shari’a Na ‘Kasa Malami Sani

Attoni Janar na Nigeria, AGF, kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya yi ikirarin cewa an yi nasarar ragargazan ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga kwarai da gaske, rahoton.
Malami ya bayyana hakan ne a birnin New York ta Amurka yayin da ya ke zantawa da manema labarai. Ya kuma yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta yi nasarar wurin ‘binciko da gano wasu manyan mutane’ da ake zargi da daukan nauyin ‘yan ta’adda a kasar.
A cewar babban jami’in doka na kasar, batun daukan nauyin ta’addanci lamari ne da ake aiki a kansa kuma baya son ya yi magana kan abin da ba a kammala bincike a kansa ba. Sai dai ya ce.
Abu daya da zan iya tabbatarwa shine, duba da irin kamen da aka yi, an karya lagwan masu daukan nauyin ta’addanci da ‘yan ta’adda don haka za a samu cigaba a bangaren dakile ‘yan ta’adda. “Kana iya gani karara cewa muna samun nasarori kan yaki da Boko Haram, wanda ke nuna cewa ana karya lagwan ‘yan ta’addan.”
Ya cigaba da cewa:
“Tuni an karya lagwan ‘yan ta’addan Boko Haram sosai kuma kana iya ganin abin da ke faruwa a yankin Arewa maso Yamma da ya shafi ‘yan bindiga.
Kada kuman Kuna Tare Dani A. Usman Ahmad a shafinmu Na Dalatopnews Dauke dalabaran Duniya.