Gwamnatin Barno Zata Hada Kai Da FG Wajan Amfani Da Mika Wuyan Yan Boko Haram

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, yace gwamnatinsa zata haɗa kai da FG wajen amfani da miƙa wuyan yan Boko Haram domin dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.

A ruhotan da manema labaranmu na Dalatopnews suka nado a yammacin yau munji cewar Gwamnan yace matakin da yan ta’addda suka ɗauka cigaba ne mai kyau kuma gwamnati ta ɗauki mataki watanni biyu da suka wuce na tallafawa miƙa wuyan yan Boko Haram da kuma dawo da zaman lafiya.

Legi.ng hausa ta rahoto cewa Zulum ya faɗi haka ne a wurin taron da ma’aikatar yaɗa labarai ta shirya ranar Alhamis, kan kayan gwamnati da aka lalata kamar hanyoyin sadarwa da wutar lantarki a Borno.

Miƙa wuyan da mayaƙan Boko Haram suke cigaba da yi, abu ne mai kyau da muke bukata. Wata biyu da suka wuce, mun ɗauki matakin amfani da wannan damar.” “Zuwa yanzun, dubbanninsu sun miƙa wuya, muna samun cikakken goyon baya daga rundunar sojoji, yan sanda, jami’an farin kaya DSS, da sauransu.

Wajen tabbatar da cimma nasara a lamarin.” “Gwamnatin Borno da FG suna aiki tare domin samar da hanyoyin da zasu taimaka wajen samun nasara, kuma shugaban ƙasa ya yi alƙawarin bada duk gudummuwar da ya kamata.

Kuna samun wannan labaran katsaye da Dalatopnews.

KU KARANTA WANNAN:

Ku Budewa Yan Ta’adda Wuta Koda Sun Shiga Cikin Mutane Cewa Gwamna Masari

Aisha Buhari Ta Samu Bakunchi Shugaban Kallon Kafar Domin Bawa Yan Mata Da Yaran Mata Damar Yin Kallo

Tirkashi Anbayyana Dalilin Dayasa Hadiza Gabon Take So Ta Auri Malam Isah Ali Pantami

 

 

Hajiya Aishatu Adamu Jagorar (NYSC) Ta Shawarci Matasa Na (NYSC) Da suyi Hakuri Su Zauna A Cikin Jahar Jigawa

 

An Yi Nasarar Ragargazar ‘Yan Boko Haram Da ‘Yan Bin Diga Acewar AGF Kuma ministan Shari’a Na ‘Kasa Malami Sani

 

Zamu iya Jin ra’ayoyinku a sahinmu na comment section Amma kafin wannan idan wannanne karanka nafarko awannan shafin munaso ku Danna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button