Hajiya Aishatu Adamu Jagorar (NYSC) Ta Shawarci Matasa Na (NYSC) Da suyi Hakuri Su Zauna A Cikin Jahar Jigawa

Jagorar hukumar matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) ta jihar Jigawa, Hajiya Aishatu Adamu, ta shawarci masu yiwa kasa hidima da aka turo jiharnan su zauna a jihar.

Aishatu Adamu ta ba da shawarar yau a jawabin maraba da ta yi wajen kaddamar da bikin wasanni da al’adu na bana a Dutse Jahar jigawa.

Ta yi bayanin cewa jihar tana da hanyoyi da yawa wadanda masu yiwa kasa hidima za su iya amfani da su domin rayuwa.

Jagorar ta kara bayyana Jigawa a matsayin jiha daya tilo wacce ma’aikatu da hukumomin gwamnati ba sa kin karbar masu yi wa kasa hidima

A nasa jawabin, Gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawa ya yabawa hukumar NYSC saboda zabar jihar a matsayin wajen gudunar da bikin wasanni da al’adu.

Gwamna Badaru, wanda Kwamishinan Yada Labarai na Matasa, Wasanni da Al’adu na jiharnan, Alhaji Bala Ibrahim ya wakilta, ya bayyana shirin NYSC a matsayin mai nagarta wanda ke cigaba da habaka hadin kai da fahimtar juna tsakanin ‘yan Najeriya. 

KAITSAYE:

Kuna sauraran wannan Daga go Dan Jarida na Dalatopnews kukasnce tare Dani A.Usman Ahmad Domin samin Labaran Duniya kada kumanta kudanna alamar kararrawar sanarwa Domin samin sabbin labaran Duniya Kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button