Hukumar (NDLEA) Ta Samu Nasarar Kama Wani Dillalin miyagun kwayoyi A Tashar Jirgin Sama

Da dimudimunsa Asafiyar yaune mukaci Kara da saban labari Wanda shafin legit.ng hausa ya Dora Ankama wani Dillalin miyagun kwayoyi A Tashar Jirgin Sama.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama wani mai suna Okey Eze, kasurgumin dillalin miyagun kwayoyi a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe, Abuja.

An damke Eze dauke da nadi 350 na hodar Iblis wanda kudin sa ya kai Naira biliyan biyu da digo uku (N2.3bn).

Hadimin shugaban hukumar, Mahmud Isa Yola, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Laraba, 22 ga Satumba, 2021. Yace Eze mai shekaru 38 kuma dan asalin karamar hukumar Oji-River, jihar Enugu ya shiga komar hukumar ne yayin da ake tantance fasinjoji kafin shiga jirgi na Ethiopian airline mai lamba 911.

 

Miyagun kwayoyin wanda nauyin su ya kai Kilograms 7.7 an nade su ne a cikin fakiti guda takwas inda ya sanya su a wurare mabanbanta a cikin kayakin da zai yi tafiya da su.

Ya kara da cewa Shugaban hukumar NDLEA, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa ya jinjinawa jami’an hukumar na reshen NAIA wadanda suka yi nasarar cafke mai laifin tare da kwayoyin Da suke  tare da shi. 

To Allah ya kyauta mun gode da sauraran wannan shiri idan wannanne karanka na far ko kada kaman ta kadannamana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button