Nayi babbar sa’a kan harkata ta fim wanda ba kowace jarumace ta isa ta sami wannan sa’ar ba, cewar jaruma Fati shu’uma

Shahararriyar kuma ficacciyar jaruma a masana’antar kannywood Fati Abubakar wacce al’umma suka saninta da Fati shu’uma, ta bayyanawa jama’a babbar sa’arta a bangaren shigarta harkar fim na kannywood shi yasa bata sha wahala ba, ta sami shiga masana’antar cikin sauki sannan kuma ficacciyar jaruma a masana’antar.

Jaruma Fati shu’uma ta bayyana hakane a shirar da sukayi da wakilin jaridar Damukaradiyya inda take bayyana cewa.

Gaskiya ina kallon kai na a matsayin wacce tashiga harkar fim cikin sauki ba tare da tasha wahala ba, domin a lokacin da nashiga harkar fim ko sati biyu banyi ba aka soma fim dani.

Sannan kuma nan take na zama jaruma a fim kafin wata biyu duk inda na shiga jama’a suna kirana domin sunganni a cikin tallan fim din, sabida haka ba kowace jarumace ta sami irin wannan sa’ar tawa ba.

Wannan batun da jaruma kannywood Fati Abdullahi wacce kukafi sani da Fati shu’uma ta bayyana, a lokacin da suke tattaunawa da wakilin jaridar Damukaradiyya.

Kamar yadda kuka sani dama ita rayuwa haka take wani yakan fi wani ko kuma sai wani ya sami daukaka daga baya wani yazo ya wuce shi, wannan jarumar Fati shu’uma ta bayyana daukakar da tasamu kan harkarta ta fim wanda da yawa daga cikin jarumai mata babu wacce ta sami irin wannan daukakar.

Da yawa daga cikin su sukan sha wahala kamin a fara sanyasu a cikin fim, wasuma sai sunbi ta wasu hanyoyin zasu sami damar shiga shirin fim wasuma sai sun biya da kudinsu.

Dama haka rayuwa take abin da kake ganin zaka sha wahala a kansa sai Allah ya kawoma sauki kaga a cimma shi ba tare da wani kalubale ba, kamar yadda jaruma Fati shu’uma ta sami daukaka cikin sauki a masana’antar ta kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button