Advertisement

Tonon asiri: Anyi ram da mawakin da yayiwa jarumar Maryam Yahaya sammu harta kwanta rashin lafiyar da takusa mutuwa

Kamar yadda kuka sami jaruma Maryam yahaya tayi fama da rashin lafiya a kwanakin baya wanda har jama’a suke tunanin ko asiri aka mata, dalilin daukakar da tasamu a masana’antar ta kannywood.

Jama’a dama sunyi mamaki kan wannan rashin lafiyar jarumar domin ganin yadda cikin dan kankanin kolaci jarumar ta rame, har ma wasu suke cece-kuce kan cewa manya-manyan jarumai da shuwagabanni na masana’antar ta kannywood sunki tallafa mata.

Wanda har shugaban hukumar tace fina-finan hausa, Alhaji Isma’ila Na Abba Afakallah, yayi magana game da cece-kucen da mutane suke na cewa sunki taimakawa jarumar.

Daga nan kuma al’umma suka rankaya kan cewa ai asiri aka yiwa Maryam Yahaya shi yasa ta kamu da wannan rashin lafiyar, inda mahaifin jarumar ya fito yayi bayani dalla-dalla yana mai cewa, Allah ne ya dorawa ‘yar sa jinya ba wani ba kuma ba asiri aka mata ba kawai rashin lafiya ce Allah ya jarrabe ta da ita.

Sai dai kuma ana tsaka da wanan cece-kuce kan rashin lafiyar jarumar sai wani Malami ya bayyana, inda ya tabbatarwa da mahaifanta cewa ‘yar tasu tana fama da bakin tsafi wanda wani abokin aikinta ya jifata da shi.

Kamar yadda Arewasocial ta ruwaito, bayan da aka mayar da jaruma Maryam Yahaya gida, sai Malamin yaci gaba da bata magani tare da yimata rukiyya da karatun Al’Qurani har Allah ya bata lafiya.

Bayan ta sami lafiya sai Malamin ya bayyana mata cewa, wani abokin aikinta ne mawaki ya jifeta da wannan sammun kuma ka tsaye rayuwarta ya nema amma sai Allah ya kare.

Malamin ya bayyana sunan mawakin daya mata sammun amma sai kungiyar Kannywood ta nemi daya sakaya sunan nasa domin gudun abin da zai biyo baya.

Ku kalli wannan bidiyon dake kasa domin kuji cikekken shirin yadda labarin yake.

Ga bidiyon nan sai ku kalla kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button