Bazan taba mantawa da abin alkairin da darakta Abdul Amart mai kwashewa ya yimin ba tare da iyalaina, cewa jarumi Bello Muhammad Bello

Jarumin masan’antar kannywood Bello Muhammad Bello ya bayyana farin cikinsa tare da yin kalamain godiya, Belllo Muhammad Bello yayi wadannan abubuwan ne sabida abin alkairin da Abdul Amart mai kwashewa yayi masa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta instagram.

Idan bazaku manta ba a kwanakin baya da suka gabata jarumi Bello Muhammad Bello ya sami kyautar Mota, wanda babban daraktan masana’antar kannywood Abdul Amart mai kwashewa yayi masa.

Darakta Abdul Amart mai kwashewa ya yiwa jarumi Bello Muhammad Bello kyaututtukan da suka ratsa zuciyarsa, domin ya taimakawa iyalansa da kuma shi Bellon kansa bayan wannan kyautar motar da yayi masa.

Karanta wannan labarin

Cin Mutunchin Da Wata Soja Tayiwa Wannan Budurwar Abun Ya Tayar Da Hankali

Jarumi Bello Muhammad Bello ya wallafa wani dan gajeren rubutu a shafinsa na instagram kamar haka.

Sunanshi Abdul Amart mai kwashewa, Abdul Amart mai kwashewa yana da mushimmanci a wajena marar musaltuwa sabisa: sai ya tsaya daga nan sannan kuma ya kara da cewa.

1• Zaki ne shi mai fita farauta, sai yayi zagaye ya samo ya rike, sannan yace duk kuzo muci tare.

2• Yana gasa kifi ya baka, amma yafiso ya jaka ya koya maka yadda ake kamun kifi.

3• Yana doraka a channel din da daya kamata kabi ka sami alziki kuma ya shige maka gaba har sai ka samu da ikon Allah, kuma baya neman kaso daga gare ka.

karanta wannan labarin

Tirkashi Yadda Miji Ya Kama Matarsa Tana Turawa Tsohon Saurayinta Hotunanta Na Tsiraichi

4• Idan zai baka kyautar gida ko mota baya dauka a waya kuma baya so a dauka a waya balle ma a nunawa duniya.

5• Wallahi bazan iya lissafa kyaututtukan da ya yimin ba daga kudade, wayoyi, motoci, kayan abinci da makamantansu.

Wannan kadan be daga cikin bayanin da jarumi Bello Muhammad Bello yayi, game da abin alkairin da darakta Abdul Amart mai kwashewa yayi masa.

kalli shirin labarina mai season 3 episode 13

LABARINA SEASON 3 EPISODE 13

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button