Jirgin Dake Dauke Da Mutane A Shirin Da Takwas 28 Yayi Hadari A GabashinRasha Wanda Babu Wanda Yarayu Acikinsu

Babu wanda ya tsira bayan da wani jirgi da ke dauke da mutane 28 ya yi hadari a gabashin Rasha a ranar Talata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Rasha ya Ambato jami’an ceto na cewa.
Jirgin mai suna Antonov 26 na kan hanyarsa daga babban birnin yankin Petropavlovsk-Kamchatsky zuwa Palana, wani kauye a arewacin tsibirin Kamchatka, lokacin da aka daina jin duriyarsa, in ji ma’aikatar bada agajin gaggawa ta Rasha.
Kamfanin dillacin labaran Rasha na Interfax ya ruwaito cewa ana tunanin jirgin ya fada cikin wani dutse ne a lokacin da yake shirin sauka a cikin wani yanayi na rashin kyawun gani.
Hukumar kula da zirga -zirgar jiragen sama ta kasar Rasha ta tabbatar da cewa an gano inda jirgin ya fadi bayan da ma’aikatar agajin gaggawa ta aike da jirgi mai saukar ungulu tare da tura tawagogi a kasa don nemansa.
Ku kasance Dani A. Usman Ahmad acikin wannan shafin na Dalatopnews Domin samin sabbin labaran Duniya.
KU KARANTA WANNAN:
An Jefa wani Jariri A Sokawe Na Bandaki A Cikin Garin Hadejia Jihar Jigawa
Gwamnatin Barno Zata Hada Kai Da FG Wajan Amfani Da Mika Wuyan Yan Boko Haram
Ku Budewa Yan Ta’adda Wuta Koda Sun Shiga Cikin Mutane Cewa Gwamna Masari
Tirkashi Anbayyana Dalilin Dayasa Hadiza Gabon Take So Ta Auri Malam Isah Ali Pantami
Mun gode da kasance was samu a wannan lokacin kucigaba da bibiyarmu a wanan Shafin namu Na Dalatopnews Kai tsaye kada kumanta kudanna alamar subscription Domin samin Jin kararrawar sanarwa mungode.