An Baliya Nafaruwa A Jamhuriyyar Nijar Wanda Kasar Nafuskantar Asara Daban-daban, Kama Daga Rayuka Har Zuwa Ta Kadarori Baki Daya.

A daidai lokacin da ake gani lokacin damuna na zuwa karshe a Jamhuriyyar Nijar, ƙasar na fuskantar asara daban-daban, kama daga rayuka har zuwa ta kadarori.

A taron majalisar ministocin ƙasar da aka gudanar, an ambato ministan kula da ayyukan agaji Laouan Magagi, na cewa mutum 70 suka rasa ransu sanadiyar ambaliyar ruwa da aka samu a dukkan faɗin kasar.

A wasu lokutan idan damuna ta yi, akan samu makamancin wannan lamari musamman idan damuna ta fara zuwa tsakiya, amma a wannan karon, ruwan ya yi ɓarna ne a lokacin da ake ganin daminar ta kusan wucewa, to sai dai Bahaushe kan ce ruwa ya yi gyara duk irin ɓarnar da ruwan kuwa ya yi.

A cewar ministan, lamarin ya shafi gidaje 25,888 inda mutum 206, 457 ba arziki suka bar gidajensu, haka kuma akwai gidaje 14,884 suka ruguje.

Haka kuma ministan ya sanar da salwanatar dabbobi manya da ƙanana, da rugujewar ban-ɗaki da azuzuwan makarantu da rijiyoyi a yankunan karkara da suka hada har da rijiyoyin burtsatse da masallatai da hanyoyi da suka cabe wasu kuma sun lalace.

Haka kuma akwai filayen noma masu yawa da suka cika maƙil da ruwa.

Zuwa yanzu dai a cewar Minista Laouan Magaji, ana da bukatar matsugunnai 14, 884, da kuma rukuni na buƙatu da ba na abinci ba 14,884.

Ta ɓanagaren bukatar abinci kuma ministan ya sanar da cewa ana bukatar tan 2,589 na abinci, da tan 130 na sukari da tan 63 na manda wato gishiri da kuma lita 12,9435 ta man girki.

A wannan lokaci dai waɗannan su ne buƙatun jama’ar da suke cikin gararin ta’annacin ambaliyar da ruwa ya haddasa a ƙasar ta Jamhuriyyar Nijar baki ɗaya.

Ko a kwanakin baya ruwan sama da aka rika sheƙawa kamar da bakin ƙwarya a ƙasar daga watan Yuni zuwa wannan watan Agusta na bana ya haifar da mummunar ambaliya da ta kashe aƙalla mutum 55 a yankunan jihar Maraɗi da Agadez da kuma babban birnin ƙasar, Yamai.

Ambaliyar ta kuma lalata gidaje aƙalla 5,000, lamarin da ya tilasta wa kusan mutun 53,000 gudun hijira, kamar yadda rahotanni suka nuna a lokacin da lamarin ya faru.

KU KARANTA WANNAN:

Tofah Bayan Mutuwar Auren Sani Danja Da Mansurah Isah Yanzu Suke Bayyana Nadamar Rabuwar Auren Nasu

Ministan sadarwa da tattalin arzikin Isa Pantami ya ce nan da watan Janairu 2022 za a fara amfani da 5G

An Jefa wani Jariri A Sokawe Na Bandaki A Cikin Garin Hadejia Jihar Jigawa

Ku Budewa Yan Ta’adda Wuta Koda Sun Shiga Cikin Mutane Cewa Gwamna Masari

Tirkashi Anbayyana Dalilin Dayasa Hadiza Gabon Take So Ta Auri Malam Isah Ali Pantami

Aisha Buhari Ta Samu Bakunchi Shugaban Kallon Kafar Domin Bawa Yan Mata Da Yaran Mata Damar Yin Kallo

Kucigaba da bibiyarmu ashafinmu na Dalatopnews kada kumanta kudanna alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu a lot da yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button