Rahotanni Daga Jihar Borno A Arewa Maso Gabashin Najeriya Na Cewa Mayakan Iswap Sun yi Wa Sojojin Kasar Kwantan Bauna A Yankin Marte-Dikwa.

Rahotanni daga jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayakan Iswap sun yi wa sojojin kasar kwantan bauna a yankin Marte-Dikwa.

Jaridar PRNigeria da ke da kusanci da sojojin Najeriya ta ce sojoji bakwai da ‘yan banga hudu aka kasha bayan Iswap ta dasa abubuwan fashewa ne domin ayarin sojoji da ke kan hanyar Maiduguri daga Marte.

Ayarin motocin sojojin na rakiyar sojojin da aka ba su izinin fita daga yankin Marte, a cewar jaridar.

Ta ce wani jami’in leken asiri ya ce an yi wa sojojin kwanton bauna ne a kusa da kauyen Ala da ke tsakanin garin Marte da Dikwa.

“Mayakan sun boye kusa da wurin suka bude wa sauran ayarin wuta, wanda ya kai ga rasa ran akalla sojoji bakwai da ‘yan banga hudu da ke cikin ayarin.”

Sai dai babu wata sanarwa daga rundunar sojojin Najeriya game da al’amarin.

KU KARANTA WANNAN:

Tirkashi wani kamfanin isra’ila Dake Sarrafa Fara Zuwa Alawoyi Da Wasu Nau’in Abinci Ya Janyo Wani Abu.

An Baliya Nafaruwa A Jamhuriyyar Nijar Wanda Kasar Nafuskantar Asara Daban-daban, Kama Daga Rayuka Har Zuwa Ta Kadarori Baki Daya.

Kotu Zatayi Hukunci Kan Karar Da Sarki Muhammad Sunusi Yakai Gwamnatin Kano

A’isha Dan Kano Tatafi Ta Dawo zee Dan Kano Na Shirin Maye Gurbin Mahaifiyarta

Rigima na shirin barkewa tsakamin Darakta Falalu a Dorayi da Afakallah kan dokar hana haska fim na ta’addanci

Innalillahi wainna’ilaihir raji’un Asafiyar yau Mika tsinkayi wani mummunan al’amari a jihar jigawa birniwa local government.

Wasu Hanyoyi Uku Da Mata Masu Juna Biyu Ke Iya Yada Wasu Cututtuka

Kada ku Manta kunatare da A.Usman Ahmad dauke da labaran Duniya Ashafinmu na Dalatop News kada ku Manta da kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu ako da yaushe.

Da wannan nake muku mukwana lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button