Rigima na shirin barkewa tsakamin Darakta Falalu a Dorayi da Afakallah kan dokar hana haska fim na ta’addanci

Kamar yadda muka kawo muku labarin cewa hukumar tace fina-finai ta gindaya doka kan wasu shirye-shiryen fina-finai da ake, wanda basu dace al’umma suna gani ba sabida a cikin fina-finai akan bayyana abubuwan da zaku kawo matsala ga rayuwar al’umma.

Sai kuma a yau muka sami labarin cewa, ficaccan jarumi kuma furodusa a masana’antar kannywood Falalu A Dorayi, yayi watsi da wannan dokar da hukumar tace fina-finan ta gindaya kan haramta yin shirin fim din da ake nuna ta’addanci irin su, kwacen waya, shaye-shaye da kuma kidinafin.

Shugaban kungiyar na tace fina-finan hausa Isma’ila na Abba Afakallah, ya bayyana mujallar fim cewa gwamnati ta dauki wannan matakin ne domin ta kare al’adar mutanen Kano da kuma mutuncin su, wanda ya bayyana hakan a ranar talata data gabata.

karanta wannan labarin

A’isha Dan Kano Tatafi Ta Dawo zee Dan Kano Na Shirin Maye Gurbin Mahaifiyarta

 

IFalalu a Dorayi wanda yana daya daga cikin wasu shirya fina-finai wanda kuma yana ganin dole wannan dokar zatayi aiki a kansa, ya bayyanawa mujallar fim cewa, kwata-kwata Isma’ila na Abba Afakallah bai yi aiki da hankalinsa ba a lokacin da zai gindaya wannan dokar.

A cikin shirar da Falalu a dorayi da mujallar fim kan wannan dokar da Afakallah ya gindaya, darakta Falalu ya fadi cewa, abin tambaya a nan shine da mai ya dogara da zai dauki wannan mataki, sannan kima ai komai za’ayi sai an tattara masu ruwa da tsaki kan lamarin sai ayi magana dasu ace ga wani abu da gwamnati zata yi, tunda kuna matsayin wandanda muke tare fina-finan da ake shiryawa ko a juya akalarsu a gayara abin da ake a ciki sabida abin ya fara ta’azzara.

karanta wannan labarin

Zan Iya Yarda Namiji Yayi Zinah Dani Sau Goma Ko Sau Sha Biyar Matukar Zai Siyamin iPhone 11 pro max Cewar Wata Budurwa

Amma kai tsaye sai kace zaka yanke hukunci a matsayinka na gwamnati, abin ya zama kamar mulkin soja kenan.

Falalu a Dorayi ya kara da cewa, ba wata doka bata bayyana cewa, baza’a harka shirin fim din shaye-shaye ba, ai haryanzu ana harka fina-fina Amurka kuma har gobe suna shirin fim akan masu tada kayar baya.

Sannan kuma suna cigaba dayin fina-finan su na ‘yan tada kayar daya wanda suke son kaiwa Amurka hari, to amma abin da ake nunawa a cikin shirin karshen wadannan mutanen baya kyau.

Daraktan ya kara da cewa, nayi tunanin abin da zan fada kan cewa duk wani fim da za’ayi na batagari idan a katshen fim din ba’a nuna wani abu da zai sami batagarin kan abubuwan da suke aikatawa, to baza’a karbi wannan shirin fim din ba wannan shine layin da za’a bi na hankali ba wai na hauka ba.

Wannan kadan daga cikin jawabin da jarumin ya bayyana kan wannan dokar da shugaban kungiyar tace fina-finai ya gindaya, Isma’ila na Abba Afakallah.

karanta wannan labarin

Tirkashi Yadda Aka Kama Wani Mutumi Yana Zinah Da Akuya

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button