Shirar Daraktan Labarina Aminu Saira kan yadda za’a cigaba da shirin Labarina season 4 da season 5 zuwa nan gaba

Kamar yadda wasu daga cikin ku suka sani Malam Aminu Saira shine daraktan shirin Labarina mai dogon zango, wanda Arewa24 da kuma tashar Youtube channel mai suna Saira Movies suke kawo muku a duk sati.
Sai kuma a wannan lokacin akayi shira da babban daraktan na shirin Labarin mai dogon zango Malam Aminu Saira, anyi shirar da shine a wajan da suke aikin cigaban shirin na Labarina season 4 da kuma season 5, wanda dama kunsan an kammala season 3 a wannan satin da yagata, sannan kuma ya bayyana ranar da zasu dawo da haska shirin nasu na season 4.
Darakta Aminu Saira ya bayyana cewa, shirin na Labarina an fara shine tun a cikin shekara ta 20214 zuwa 2015, wanda shahararan marubucin nan mai suna Ibrashim Birniwa ya rubuta daga zango na daya zuwa zango na biyu, sannan kuma sai aka shigo da sabbin marubuta a cikin saurarrakin zangunan da za’ayi nan gaba.
karanta wannan labarin
Zamu Dauki Mummunan Mataki Akan Abunda Akayiwa Adam A Zango
Haka kuma darakta Aminu Saira ya bayyana abin da yafi birgeshi game da wannan shirin nasu na Labarina, yadda al’umma manya da yara suke kallon shirin Labarina kamar da gaske, sannan kuma yace har furufesas suna kiransa suna yi masa martani akan shirin fin din nasa na Labarina, inda Aminu Saira yace shi hakan da ake masa yana sanya shi farin ciki kuma yana burgeshi.
Domin kuji cikekkiyar shirar da akayi da shi sai ku kalli bidiyon dake kasa, sannan kuma muna bukatar ku danna alamar subscribe domin samin cigaban wasu labaran namu.
Ga bidiyon nan sai ku kalla kai tsaye.
karanta wannan labarin
Nasha Gamuwa Da Masu Sha’awar Lalata Dani A Kannywood Cewar Nafisa Salisu Jarumar Macen Sirri