Tirkashi wani kamfanin isra’ila Dake Sarrafa Fara Zuwa Alawoyi Da Wasu Nau’in Abinci Ya Janyo Wani Abu.

Wani kamfanin Isra’ila na fatan zama kan gaba wajen wannan rikita-rikitar ta hanyar sarrafa su ta wata fuska ta daban.

Dror Tamir ya buɗe wata takarda launin ruwan kasa, sai yaga alawar jellied sweets. “Ka dandana guda,” ya kuma yaba wa kamfanin abinci na Hargol.

‘Yan kananan alawar mai danko an naɗe ta ne a takarda, sai dai ba yadda aka saba yin su ba da waken suya ko kuma mai abubuwan da ake yin biskit da su. An naɗe su cikin wani abu mai kyau wanda zai yi dadin ci, da aka yi da ƙwari masu tashi – irinsu fara.

Yanayin dandanon fara da nau’ukanta sun yi kama da na gahawa da cakulati da kuma kamar gyada,” in ji Mista Tamir. “Amma saboda muna da nau’ukan abinci za mu iya kara masa dadi… alawowin za a rika yinsu ne da dandanon lemon fata da kuma Strawberry.”

Ɗan kasar Isra’ilar ya ce yana da son fara tun yana ɗan yaro karami, bayan jin labarin fara daga wajen kakarsa ta wajen mahaifiya, wadda ta rika yin girki a lokacin kibbutz, a wata gonar gandu.

“Na koyi hakan ne tun a shekarun 1950, lokacin da Isra’ila ta yi fama da karancin abinci da kuma kwararar fari da aka samu daga Afrika wadanda suka lalata amfanin gona,” kamar yadda ya ce.

“Da yawan mutanen kibbutz sun rika bin farin aguje suna korarsu, Yahudawan Yemen da na Moroko sun rika kwasarsu tantan suna ci.

A lokacin ne na fuskanci ashe fara abincin biliyoyin mutane ce a duniya.”

Da mu tuni mutanen Afrika da Asiya da gabas ta tsakiya da tsakiyar Amurka suka saba cin ƙwari, amma a wurin Turawa da na arewacin Amurka hakan ba wani abin sha’awa ba ne.

Sai dai Tamir na fatan sauya duka wadannan abubuwa, kuma kamfaninsa na fatan samar da wasu kayayyaki na daban. Bayan alawar zai samar da wasu alawowin masu kara kuzari da dai sauransu.

Idan har yanzu kana jin cewa ƙwari ba sa cikin abincin mutanen yammaci, to wasu masana na ganin cewa lokaci zai zo da ba mu da wani zaɓi saboda yadda za a lura da muhalli da kuma karin yawan al’umma da ake samu a duniya.

Mista Tamir ya gamsu da cewa dalilin kula da muhalli da na lafiya sun isa su mayar da ƙwari abinci.

Kamfaninsa da ke arewacin Isra’ila na kiwon fari a wani rufaffen wuri da aka gina aka sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana. Mafi yawansu suna haihuwar irin farin da suke yin hijira ne daga Afrika.

“Za mu iya samar da fari miliyan 400 a gonarmu a shekara,” in ji Tamir, wanda ya kara da cewa a kwanaki 29 ne kawai ƙwarin suke girma yadda ake so.

Ya ce idan aka kwatanta da noman kudan zuma, noman fara yana rage hayaƙin da ake fitarwa da kashi 99 cikin 100.

Tamir ya kuma nuna cewa fara abinci ne da ya halarta da Yahudawa da kuma Musulmai.

New Economy wani sabon harkar kasuwanci ne da ke nuna yadda kasuwanci ke habbaka da kuma sauyawa a rayuwa cikin gaggawa.

________________________________

Za dai ka iya sayan wadannan ƙwari domin ka ci, ya danganta da a wace kasa mutum yake zaune. A Burtaniya za ka iya sayansu ta Intanet daga kamfanonin da suke dillancinsu, a yanzu haka ma kamfanonin na kokarin ganin yadda gwamnati za ta rage wasu tsarafe-tsarafe da ke tattare da kasuwancin.

To Allah ya Kyauta Zakuiya samana ra’ayoyinku a sahinmu na tsokaci danjin tabakinku .

LABARAI MASU ALAKA:

An Hana Sanya Matsatstsun Kayan Da Basu kamata Ba A Jami’ar Adekunle Ajasin Ta Jihar Ondo

‘Yan Okada Sun Kashe Wani Jami’in Dansanda A Jahar Legos Maisuna kazeem S Abonde

Gaskiyar labari game da soyayyar Sheikh Isah Ali Pantami da jarumar kannywood Hafiza Aliyu Gabon

Jirgin Dake Dauke Da Mutane A Shirin Da Takwas 28 Yayi Hadari A GabashinRasha Wanda Babu Wanda Yarayu Acikinsu

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani tsohon dan majalisar jihar, Mr Joseph Adegbesan da wasu mutane 2 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri

Kada kumanta kuna tare Dani A.Usman Ahmad kaitsaye ashafinmu na Dalatopnews kada kumanta kudanna alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button