Wasu Hanyoyi Uku Da Mata Masu Juna Biyu Ke Iya Yada Wasu Cututtuka

Wannan ci gaban na makon da ya gabata ne, kuma an tattauna ne da wata kwararriyar likitar mata Dr Mairo Mandara.
Wasu hanyoyi uku da mata masu juna biyu ke iya yada wasu cututtuka zuwa ga jariransu su ne, a ciki da lokacin haihuwa da kuma yayin shayarwa, in ji likitoci.
Wadannan cututtuka suna da dama, amma wasu daga cikinsu su ne, ciwon hanta, cutar sanyi, cutar Tetanus, cutar karambau da kuma cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya.
Kungiyar kwararrun likitocin mata ta Amurka, ACOG, ta bayyana cutar HIV da cewa tana daya daga cikin cututtukan da uwa ke yadawa zuwa ga danta.
Daya daga cikin manyan hanyoyin da ake daukar kwayar cutar HIV dai shi ne ta hanyar jini.
Haka kuma da zarar kwayar cutar ta shiga jini sai ta mamaye kwayoyin halittar da ake kira CD4, a likitance.
Wadannan kwayoyin halittun su ne jiga-jigan garkuwar jikin dan adam.
Saboda haka, sai garkuwar ta yi rauni kuma jiki ya kasa yaki da kwayoyin cututtukan da za su kama mutum.
ACOG ta ce akwai wasu hanyoyin wadanda idan mace mai ciki kuma mai HIV ta bisu, to akwai yiyuwar kashi 99 cikin dari ba za ta yada cutar ga jaririn taba.
Nasha Gamuwa Da Masu Sha’awar Lalata Dani A Kannywood Cewar Nafisa Salisu Jarumar Macen Sirri
inji Ubanwa Yace Da Tuni Kannywood Ta Lalace Ba Domin Affakallahu Ba Cewar Bello M Bello
innalillahi Kalli Rashin imani A Wajen Wannan Mai Garkuwa Da Mutanen
A’isha Dan Kano Tatafi Ta Dawo zee Dan Kano Na Shirin Maye Gurbin Mahaifiyarta
Kucigaba da kasancewa da A.Usman Ahamd ashafinmu na Dalatopnews kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar sanarwa shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.