Alhaji Abdussamad mai kamfanin BUA ya baiwa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero kyautat motar Naira Miliyan dari biyu 200M kirar Roll-Royce

Wasu majiyoyi daga fadar masarautar jihra Kano sun tabbatarwa da Hauda Daily Time, saukar motar Sarkin jihar Kano Aminu Ado Bayero.

Sarkin jihar Kano Aminu Ado Bayero ya sami kyautar dalleliyar mota wanda kowa ya ganta sai ya yaba ta, sabida motar ta alfarma ce kuma ta shiga taro.

Motar da aka baiwa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, motar kirar Roll-Royce Phantom ce, sannan kuma irinta ce wanda Sarkin Kano na 14, Khalifa Muhammad Sunusi na II yake hawa, tun bayan daya sauka daga karaga har kawo yanzu.

Karanta wannan labarin

Yadda Rayuwar Wata Budurwa Ta Lalace Bayan Tashigo Masana’antar Kannywood Cewar Aminu S Bono

Darajar kudin wannan motar da aka baiwa Sarkin Kano Aminu Ado Bayeto zai kai kimanin Dalar$ Amurka $455,000 zuwa $535,000, wanda idan aka lissafa kudin da Naira zai kai kimanin Naira Miliyan (N187m zuwa N219,8m).

Shugaban kamfanin BUA Alhaji Abdussamad ya tabbatar da wannan kyautar motar ta Miliyan dari biyu kirar Roll-Royce, ga Sarkin Kano Aminu Ado Bayero.

Ga hoton motar nan a kasa sai ku kalla domin kuga irin kyawunta.

Karanta wannan labarin

Tirkashi Wata Sabuwa Musulunci Bai Haramta Min Auren Hadiza Gabon Ba Cewar Malam Isah Ali Pantami

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button