Babban sako zuwa ga Gwamnatin Jihar Kano kan daina haska fina-finan shaye-shaye, kidinafin, kwacen wayoyi

Kamar yadda muka kawo labarin cewa za’a dakatar ta haska shirin fina-finai wadanda ake nuna harkar daba da shaye shaye da kuma kwacen wayoyi, wanda hukumar tace fina-finan ta jihar Kano zata zartar.

Sai a yau muka sami wata bidiyo wanda ficaccan Malamin addini Asadus Islam yake bayyana cewa, ‘yan fim suna taimakawa Yahudu wajan yakar al’umma da kuma ruguje Arewacin Nageriya ya kamata idan basu sani bama to su sani.

Dama har kullum Malamin yakan fadi gaskiya kan abubuwan da basu dace ba idan yaga ana aikatawa, shine a yanzu ma Malamin ya cire tsoro ya fadi dukkan abin da yadace a cikin wannan bidiyo kamar yadda zakuji.

Karanta wannan labarin

Wasu Hanyoyi Uku Da Mata Masu Juna Biyu Ke Iya Yada Wasu Cututtuka

Wasu daga cikin jaruman kannywood wanda aka sami damar zantawa dasu kan wannan al’amarin, sai kamar suke nuna rashin goyon bayansu kan al’amarin kamar yadda zakuji a cikin bidiyon idan kuka kalla.

Ficacciyar jaruma kuma wanda ake daukanta a natsayin Uwa a masana’antar ta kannywood, Saratu Gidado wanda aka fi saninta da Saratu Daso, ta bada goyon baya dari bisa dari kan wannan dokar da za’a gindaya kan haska fina-finan da basu dace ana haskasu ba.

Inda Saratu Daso take cewa: Kwarai naji dadin wannan dokar da aka gindaya game da dakatar da fina-finan da ake nuna shaye-shaye, kwacen waya ko kidinafin, dalili shine yaran da muke dasu karamar kwakwalwa garesu idan suna kallon wannan shiri zasu iya kwaikwayarsa, amma idan manya ne dama sun san wannan shirin wasan kwaikwayo ne.

Ta kara da cewa inda matsalar tace shine, duk fina-finan da ake shiryawa manya suna kalla kuma yara ma suna kalla, sabida haka masu karamar kwakwalwa zasu iya yin koyi da wadannan abubuwan da ake a cikin shirin fina-finan.

Karanta wannan labarin

Bani Da Burin Daya Wuce Na Auri Mata Hudu Lokaci Guda Idan Zanyi Aure Cewar Malam Tsalha Na Shirin Dadin Kowa

Wasu daga cikin jaruman masana’antar kannywood sun amince da wannan dokar da za’a gindaya, sabida suna ganin hakan da za’a yi yana da matukar mushimmanci a tsakanin al’umma musamman ma a wannan lokaci da muke ciki.

Ku kalli bidiyon dake kasa domin kuji yadda Malamin yayi da kuma shirar da akayi da wasu jaruman kan dai na haska fina-finan da basu dace ba.

Sannan kuma muna bukatar ku danna alamar sunscribe domin samin wasu labaran namu ako da yashe.

Ga bidiyon nan sai ku kalla kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button