Advertisement

Batun Hana Fina-finan Shaye-shaye Da Ta’addanchi Yanzu Wata Rigimar Ta Sake Barkewa A Kannywood

Idan Baku Manta Ba A Yanzu Ana Tsaka Da Tattauna Batu Akan Hana Duk Wani Film Da Yake Da Alaka Da Shaye-shaye Ko Daba Gami Da Kwacen Waya Ko Sata A Kannywood Yadda Har Wasu Daga Cikin Jaruman Suke Ganin Hakan Bai Dace Ba Yanzu Wani Sabon Al’amari Ya Sake Bulla.

Kamar Yadda Bayanin Wani Jarumi Ya Fara  Wanda Muka Samo Asalin Labarin Daga Shafin Fimmagazine Sun Wallafa Bayaninsa Kamar Haka;

DA farko dai a fahimta ta da kuma ɗan ilimin da Allah ya ba ni daidai gwargwado a kan wannan harka ta fim, ban ga laifin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano a kan dakatar da nuna garkuwa da mutane, shaye-shayen ƙwayoyi da ƙwace waya a fim ba. Idan mun duba tare da bibiya, ita kan ta Gwamnatin Tarayya ta kafa hukumomi masu kula da wannan ɓangare ta hanyar inganta sana’ar da masu yin sana’ar. Gwamanti ta yi tanade-tanade masu yawan gaske a kan hakan.

Amma saboda rashin bibiya ko kuma in ce ƙarancin bincike a kan tanadin da waɗannan hukumomi su ka yi mana tun kafin mutum ya fara wannan sana’a su ne dalilan da su ka janyo a duk lokacin da wata hukuma ta bijiro da wata doka domin kawo gyara, ko kuma da ma da akwai wannan doka amma ana son a inganta ta, to daga jin haka sai ka ji an fara ce-ce-ku ce, kowa na faɗin ra’ayin sa, wanda wannan ra’ayi nasa ya saɓa wa dokar, amma fa shi mai yin ƙorafin ya na ganin shi ke da gaskiya alhali ba haka ba ne.

Akwai kundin tsarin yadda Gwamnatin Tarayya ta rubuta hanyoyin da duk wani mai son shirya fim a wannan ƙasa zai bi domin gudanar da harkokin sa. Ya na nan cikin ‘National Film Policy’. Wannan kundi ya hana nuna abubuwa da dama waɗanda su ka jiɓinci fito da tsirarar aikata wasu laifuka manya da ƙanana a fili. Wannan kundi ya haramta nuna abubuwan da ake ta ce-ce-ku-ce a kan su. Amma sakaci na hukumomin da alhakin ya rataya a kan su da son zuciya da rashin zuba ƙwararru su zamo su ne masu kula da waɗannan ɓangarori ya janyo mafiya yawan masu shirya fim su ke ganin abin kamar wani sabo ne. Babu sabunta cikin dokokin da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta yi bisa wannan batu da mu ke ganin ba a kyauta ba.

Ya na da kyau ‘yan’uwa masu wannan sana’a su ƙara faɗaɗa binkice da neman ilimin abin da ba su san shi ba. Kuma su dinga yi wa dokoki da ƙa’idojin sababbi da tsofaffi kallo da idon basira.

Menene laifi don an ce kar mu fito ƙarara mu nuna aiwatar da laifuka a zahiri a halin da ƙasar mu ta tsinci kan ta na rashin tsaro da sauran nau’ika na ta’addanci kala-kala? Ai ya kamata a ce ko cewa aka yi mu dakata da shirin fim a yanzu idan har dakatarwa za ta kawo mana sauƙi cikin al’amura, to mu dakata ɗin.

Idan ni ɗan fim ko mai shirya fim na yarda da cewa mutane na fa’idantuwa idan sun kalli fim ɗin mu, to dole kuma mu yarda cewa idan mu ka saka saɓanin hakan wasu za su iya koyon aikata sharri ko wasu su koyi rashin tarbiyya.

Ba kowa ba ne ya san cewa don ka nuna aikata laifi da masu aikata laifin a cikin fim kafin ka zo ka nuna sakamakon su a ƙarshen fim ba sai nadiran. Ba kowa ba ne ya san cewa kowane fim akwai irin rukunin mutanen da aka shirya wa fim ɗin. Haka ba kowa ba ne ya san cewa hukumomin tace finaifinai su na da ‘classification’ na shekaru ga masu kallon fim.

Da yawan mu sun sani cewa duk wani fim da aka shirya akwai rukunin shekarun mutanen da ake so su kalla kuma an yi fim ɗin ne domin su. Saboda haka, ƙarancin masaniyar haka ta sa masu kallon lamarin ba a dai ɗdai ba su ka fi yawa.

Amma fa a wani ɓangaren dukkan mu mun san cewa shiriya ta Allah ce  amma tarbiyyantarwa ta mutum ce. Allah kaɗai ke bada shiriya, shi ya ke shiryar da wanda ya so, ya ɓatar da wanda ya so.

Tun kafin finafinan Hausa su haɓaka babu irin fim ɗin da ba mu gani ba da ‘yan daba, da shaye-shaye iri daban-daban da sace- sace, finafinai irin na ‘Dakuu’, amma mu ba mu koya ba. Allah bai so mu ɓata ba ta dalilin kallon fim.

Idan fim ɗin Hausa na ɓatarwa, to na ƙasashen ƙetare ma na ɓatarwa, duk da cewa fa mun yarda da cewa shiriya ta Allah ce ba wanin sa ba. To ina imanin mu ya ke a nan kenan?

Haƙƙin mu ne mu yi ƙoƙari mu nuna muhimmacin aikata alheri, kuma mu nuna illar aikata sharri.

Tun ran gini tun ran zane! Afakalla ya ɓata rawar sa da tsalle ta hanyar ɓatawa da mutane da dama da su ka fito daga wannan masana’anta. Da yawa mutanen da su ka taimake shi a rayuwa da ‘yan ga-ni-kashe-nin-sa sun ɓata, har da ni kai na! Afakalla ya janyo na yi asarar kuɗaɗe masu yawan gaske, kama daga kwamitin gyaran kasuwa da hukumar ta kafa kuma aka ba ni shugabancin kwamitin da kuɗaɗe na ko kuma in ce kuɗaɗen aljihun mu mu ka aiwatar da wannan kwamiti.

Babu yadda za a ce hukuma ta kafa kwamiti amma ba a ba su kuɗin zama ko zirga-zirga da sadarwa da buga takardu ba. Amma saboda ganin shi namu ne kuma  mun yi zaton dukkan mu za mu amfana da ƙudirin da aka ɗora mana nauyi, daga ƙarshe haka mu ka ɓaɓe.

‘Yan’uwa Dangantaka ta Afakallah da sanin ko ni waye a ɓangaren shirin fim  ta yi ƙarfin gaske, duk da alaƙa ta da Afakallahu amma ya riƙe mun satifiket, har yanzu bai ba ni ba Fim ɗin da na kashe wa miliyan 1.8 mai suna ‘Wuta  A Maƙera’ saboda a cikin fim ɗin wani dattijo ya zagi wani yaro, don yaron ya yi ƙarya dattijon ya ce, “Yanzu wannan shegen yaron cewa ya yi daku ɗan’uwan ta ne?” Sai aka ce sai na cire kalamin “shegen yaron”, ni kuma na ce masa   bisa zamantakewa ta Malam Bahaushe iyaye ko manya su na zagin na ƙasa da su cikin fushi. To, har yau shiru ka ke ji tun 2018.

To Kunji Abunda Jarumin Ya Fada Tare Da Nuna Rashin Goyon Bayansa Akan Wannan Al’amari.

Zamu So Mu Karbi ra’ayoyinku A Sashenmu Na Kwamen.

Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan:

Babban sako zuwa ga Gwamnatin Jihar Kano kan daina haska fina-finan shaye-shaye, kidinafin, kwacen wayoyi

 

Ku Karanta Wannan:

Bani Da Burin Daya Wuce Na Auri Mata Hudu Lokaci Guda Idan Zanyi Aure Cewar Malam Tsalha Na Shirin Dadin Kowa

 

Ku Karanta Wannan:

Shirar Daraktan Labarina Aminu Saira kan yadda za’a cigaba da shirin Labarina season 4 da season 5 zuwa nan gaba

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button