Yadda Rayuwar Wata Budurwa Ta Lalace Bayan Tashigo Masana’antar Kannywood Cewar Aminu S Bono

A Kwanakin Baya Ne Fitaccen Jarumi A Masana’antar Kannywood Wato Aminu S Bono Ya Bayar Da Labarin Wata Budurwa Yadda Rayuwarta Tashiga Wani Hali Marar Kyau A Sanadiyyar Son Harkar Film Din Hausa.

Acikin Bayani Ya Bayar Da Labarin Cewa Wani Abokinsa Ne Ya Bayyana Masa Gaskiyar Lamari Akan Rayuwar Wannan Yarinyar.

Bayaninsa Ya Fara Kamar Haka;

Cikin watan December na shekarar data wuce waniabokina Wanda mukayi makaranta tare ya kirani a
waya yace in fadi duk inda nake zaizo ya sameni, na
gaya masa cewa ina wani waje haka yaje ya sameni.

Ya fito daga mota muka gaisa, daman jamiin tsaro ne
sai yace dani suna aiki a kan babban titin shigowa
Kano sai suka hadu da wata yarinya tazo tace bata
San kowa ba a Kano kuma zuwa tayi domin ta fara
Hausa film.

Sai yaje ya bude kofar motar Sai naga yarinya ta fito,
doguwa, yar fulani, Amma ba fara bace, kana ganinta
kaga ‘yar kauye saboda gaba daya tsoron mutanetake a lokacin.

Abokin nawa yace da ita wannan shine Wanda nake
gayamiki Kuma yana harka da ‘yan film saboda haka
Sai ki sake yi masa bayani.

Zai tafi Sai ya bata dubu biyu yace Sai ta hau mota.Na rasa me zance da wannan yarinyar, Sai nace mata kiyi min bayani tsakaninki da Allah me yasa kika baro gida kika tawo Shiga harkar film.

Yarinya ta fara bani labarin cewa iyayenta sun rabu Kuma tana wajen kishiyar babarta Amma tana dukanta tana bata wahala, bata samun tana ci Kumaidan ta gayawa baban nata baya yarda da wahalar datake shaaHaka dai ta gama bani labarin irin rayuwar nan dai dayara suke shiga a hannun kishiyoyi musamman idan

mahaifiyar yaro bata gidan.Na bata shawara nace ta koma gida ai yanzu anahutun kirsimeti dana sabuwar shekara saboda hakaana hutu idan an gama hutun zan kirata.

Yarinyar nan dai ta tafi Garinsu, na sakata a cikin
mota na biya mata kudin mota ta tafi gida ta karbi
number waya ta.Bayan wajen wata daya Sai naji Kiran waya, tayi min
bayani sosai har na gane ta, sai tace yanzu tana Kand
nace bana kusa tace zata jirani in dawo. Da yamma
wajen karfe biyar muka hadu da ita.Sai na tambaye ta wai me yasa ita dole Sai ta shigaharkar film? Shine tace dalili na farko tana son itamata dinga saka manyan Atamfofi da leshi da shaddodi
irin yadda irinsu Maryam Yahaya suke sakawa.

Sannan tace tana son ta shiga harkar film saboda ta
samu kudi ta dinga kaiwa mahaifiyar ta kayan dadi deAtamfofi masu tsada.Sannan tace tana son film saboda ta dinga kwana ahotel kawai tana more arzikinta.A karshe tace tana son tayi suna idan taje waje a
dinga daukar.

Toh Allah Ya Kyauta Zamu So Mu Karbi Ra’yoyinku Akan Yadda Yam Matanmu Na Yanzu Suke So Su Lalata Rayuwarsu Idan Har Zasu Samu Damar Shiga Masana’antar Kannywood.

Ku Karanta Wannan:

Batun Hana Fina-finan Shaye-shaye Da Ta’addanchi Yanzu Wata Rigimar Ta Sake Barkewa A Kannywood

 

Ku Karanta Wannan:

Babban sako zuwa ga Gwamnatin Jihar Kano kan daina haska fina-finan shaye-shaye, kidinafin, kwacen wayoyi

 

Ku Karanta Wannan:

Bani Da Burin Daya Wuce Na Auri Mata Hudu Lokaci Guda Idan Zanyi Aure Cewar Malam Tsalha Na Shirin Dadin Kowa

 

Muna so Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button