Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya fadi matakin da zai dauka kan almajirai masu karatun Alkur’ani

Gwamnan jihar sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa, Gwamnatinsa zata kawo gyare-gyare a bangaren makarantun alma’irai.
Sannan kuma Gwamnan ya kara da cesa, babu wani dalili da zai sa Gwamnatinsa ta hana karatun naiman ilimin addinin Alkur’ani mai girma a jiharsa ta Sokoto.
Haha kuma Gwamnatin tarayya ta yaba wannan tsarinn na Gwamnan Sokoyo Aminu Waziri Tambuwal, kan wannan gudanar da gyaran da zai yi.
Karanta wannan labarin
A lokacin da Gwamnan yake bayani a ranar Asabat, a wajan rufe taron karawa juna sani game da wadannan makarantun na almajirai.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yace, Gwamnatinsa zatayi iya bakin kokarinta game da wannan gyara da za’a gudanar kan makarantun almajirai.
Karanta wannan labarin
mayaƙan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Babban Gida da ke ƙaramar hukumar Tarmowa a jihar Yobe.
Gwamnan ya kara da cewa, bamu da kudurin hana karatun karatun haddar Alkur’ani wanda almajirai suke a tsangaya, domin kuwa har wasu mutane sun fara baiwa Sokoto shawara tabi sahu irin na sauran jahohi kamar yadda sukayi.
Ya kara da cewa, muna iya bakin kokarinmu wajan ganin mun nemo hanyoyin da za’a warware dukkan wani kalubale da karantun tsangaya yake fuskanta, sannan kuma munyi damarar yin hakan domin lokaci yayi.
Gwamnan ya kara da cewa, gudanar da gyararrakin da za’a ayi na makaramtar almajirai, zai taimaka wajan ganin yaran sun rage gararanba ba tare da zuwa makaranta ba.
Karanta wannan labarin
Tonon Asiri Ashe Akwai Hadin Bakin Wani DPO Akan Garkuwa Da Mutane Yanzu Gaskiya Ta Bayyana