Kwantan Baunar Da ‘yan Boko Haram Suka Kai Sun Kashe Sojojin Nigeria Mutum Bakwai Da ‘Yan Sakai Hudu A Jihar Barno

A yammacin yau muka Sami wani rahoto daga shafin BBC Wanda suke cewa ‘yan Boko Haram sun kashe wasu sojoji Guda bakwai da ‘yan Sakai Hudu bayan  wani Garin kwantan bauna da sukayi musu.

Rahotanni daga Najeriya na cewa kungiyar Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya bakwai da ‘yan sa kai hudu, bayan wani harin kwanton bauna a tsakanin karamar hukumar Marte zuwa Dikwa a jihar Borno, da ke arewa maso gabashin kasar.

Wasu majoyoyi sun ce daya daga cikin motocin da ke cikin kwambar sojojin ce ta taka wani abun fashewa da aka binne a kasa, nan take ta tashi.

Majiyoyin tsaro sun ce jim kadan bayan fashewar ne kuma mayakan suka rika harbo manyan makamai ga motocin jami’an sojin.

Ba wannan ne karon farko da aka kashe sojojin kasar a harin kwanton bauna a yankin da Boko Haram ta yi sansani ba, don ko a watan Afrilun da ya gabata ma an kashe wasu da dama, bayan da motarsu ta taka wani bom da aka dana a karkashin kasa a jihar Bornon.

Haka zalika yanzuma Kuna tare Dani A.Usman Ahmad dauke da labaran Duniya daga shafinmu na Dalatopnews.

KU KARANTA WANNAN:

An Biya kudin Fansan yaran Da A kayi Garkuwa Dasu A Jihar Kaduna.

Ya kamata jama’a suyi koyi da irin halin wannnan matashin yaron domin gamawa da duniya lafiya da samin babban rabo a lashira

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya fadi matakin da zai dauka kan almajirai masu karatun Alkur’ani

Tirkashi Yadda Dakarun Sojojin Kasar Niger Suka ceci Sojojin Nigeria 9 Wanda ‘yan Bindiga Suka farmusu.

Ku cigaba da bibiyarmu a shafinmu na Dalatopnews kada kumanta ku Danna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button