Tirkashi Yadda Dakarun Sojojin Kasar Niger Suka ceci Sojojin Nigeria 9 Wanda ‘yan Bindiga Suka farmusu.

Dakarun sojin kasar Nijar sun ceci sojojin Najeriya 9 wadanda suka tsere yayin da ‘yan bindigan daji suka far musu a Sokoto. 

A safiyar yau muka tsinci wani labar daga shafin legit.ng hausa Wanda suke bayyana Mana yadda sojojin Niger  suka ceci sojojin Nigeria a hannun yanta Adda.

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa an ceci sojin Najeriyan a Basira, wani kauye da ke kan iyaka karkashin yankin Hodan Roumdji a jamhuriyar Nijar a ranar Juma’a. 

Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka kai farmaki sansanin hadin guiwa na sojoji da ke sansanin Burkusuma a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto inda suka kashe jami’an tsaro da Dama.

Duk da an kai farmakin a sa’o’in farko na ranar Juma’a, ba a samu bayanai ba har sai ranar Lahadi saboda datse layikan sadarwa a jihar Zamfara da wasu sassan Sokoto da Katsina.

Dan majalisar jihar Sokoto a matakin jiha, Aminu AlMustapha Gobir, ya tabbatar da farmakin inda yace jami’an tsaro 12 sun rasa ransu.

Hakazalika, kwamishinan tsaro na jihar, Kanal Garba Moyi mai ritaya, ya tabbatar da harin ga Daily Trust amma ya ce bai san yawan wadanda aka rasa ba.

Daily Trust ta tattaro cewa, miyagun ‘yan bindigan da suka kai farmakin sun hada da na kungiyoyi biyu na jiga-jigan ‘yan bindigar Zamfara irin su Halilu Sububu da Kachalla Turji. 

To jama’a Kuna samun labaraine da Nan shafinmu na Dalatopnews sannan Dani Kuma like tare A.Usman Ahmad dauke da labaran Duniya.

KU KARANTA WANNAN: 

Tonon Asiri Ashe Akwai Hadin Bakin Wani DPO Akan Garkuwa Da Mutane Yanzu Gaskiya Ta Bayyana

mayaƙan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Babban Gida da ke ƙaramar hukumar Tarmowa a jihar Yobe.

Alhaji Abdussamad mai kamfanin BUA ya baiwa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero kyautat motar Naira Miliyan dari biyu 200M kirar Roll-Royce

Tarbar Muhammad Baban Dede Hadejia Wanda Ta bawa Jama’ar jihar jigawa mamaki

 

Tirkashi Wata Sabuwa Musulunci Bai Haramta Min Auren Hadiza Gabon Ba Cewar Malam Isah Ali Pantami

Kad kumanta ku danna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button