Tsananin Kyau Na Ya Sanya Maza Ke Guduna Har Yanzu Bani Da Saurayi Cewar Hauwa

Budurwa Ta Shiga Damuwa Matuka Akan Yadda Samari Ke Gudunta Maimakon Sun Dinga Rububin Zuwa Wajenta
Budurwa Mai Suna Tace Ta Rasa Dalilin Da Ya Sanya Mazan Suke Ta Faman Gudunta Saboda Tsananin Kyawun Da Allah Yayi Mata
A Wani Rubutu Da Ta Wallafa Da Yake Ta Faman Yawo A Shafukan Sada Zumunta Kyakkyawar Budurwar Ta Bayyana Rashib Jin Dadinta Akan Kyawun Da Take Dashi Inda Tace Shine Babban Dalilin Da Ya Sanya Har Yanzu Bata Da Saurayi
Tace A Lokuta Da Dama Samari Sukan Turo Mata Sako Na Cewa Suna Sonta Kuma Zasu Kari Rayuwarsu Da Ita Amma Da Abu Yayi Nisa Sai Su Gudu Baza Ta Kara Ji Daga Karesu Ba
Tsoron Su Kada Sai Suna Cikin Soyayya Dani Wani Yazo Ya Kwace Ni Hakan Ya Sanya Suke Jin Tsoro Kuma Suke Guduwa
Sunce Kyawuna Yana Basu Tsoro Saboda Namiji Kan Iya Zuwa Ya Daukeni Kuma Hakan Ya Sanya Basa Jin Zasu Iya Cigaba Da Soyayya Dani Hauwa Ta Wallafa Cewa “Lokacin Da Ta Fara Girma Ta Samu Mutane Da Yawan Gaske Da Suka Nuna Soyayyarsu A Kanta Amma Da Ta Girma Yanzu Sun Gudu
Dana Fara Girma Mutane Suna Matukar Sona Kuma Suna Kula Dani Sosai Har Ya Sanya Ni Jin Dadi Cewa Ina Da Matukar Masoya Amma Da Na Cika ‘Ya Mace Sai Na Gano Cewa Kyauna Bashi Da Wani Amfani
Tace Tana Ji Tan Gani Sa’anninta Suke Yin Aure Amma Ni Hakan Ya Gagara Maza Ko Da Yaushe Suna Nesanta Kansu Dani Suna Cewa Kyauna Yayi Yawa Inda Suke Cewa Sun Tabbata Suna Ji Suna Gani Wani Zai Zo Ya Kwaceni Saboda Sun Tabbata Idon Mutane Da Yawa Yana Kaina Saboda Haka Da Wuri Za’a Iya Kwaceni
Ku Karanta Wannan Labarin
Sunana Hauwa Daga Jihar Adamawa Ni Kuma Bafulatanace Kamar Yadda Daily News Hausa Suka Wallafa Wannan Labarin.