Yadda Amarya Ta Gudu Lokacin Daurin Aure Bayan Ta Gano Mijin Dazata Aura Direban Motar Haya Ne

Kamar Yadda Kuka Sani Dai Aure Shine Ginshikin Rayuwar Dan Adam Ta Wata Sigar, Yadda Kafin Ayi Aure Ana Iya Ganin Mutane Biyu Wato Mace Da Namiji Sun Fahimchi Junansu Har Suyi Sha’awar Zama Tare Domin Jin Dadin Rayuwa A Kadaice.
Baya Da Haka Kafin Aure Saurayi Ko Budurwa Sukan Iya Fukantar Al’amarinsu Wajen Sana’ar Da Saurayin Yakeyi Domin Zaton Samun Jin Dadi Da Kwaciyar Hankali idan Anyi Auren, Har Wani Lokaci Iyaye Sukan Iya Bincike Akan Sana’ar Wanda Zai Auri ‘yarsu Domin Ganin Rayuwarta Ta Inganta.
Toh A Yau Kuma Sai Muka Tashi Da Wani Labari Kamar Haka;
Wani abin dariya da ban mamaki da ya faru a wani kauye mai suna Kilifi dake kasar Kenya ya sanya mutane na tofa albarkacin bakin su, bayan amarya ta gudu daga wajen daurin auren su yayin da ta gano cewa mijin ya shirga mata karya.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, angon ya bayyanawa amaryar cewa shi ma’aikacin banki ne, hakan ya sanya ta dauki karan so ta dora masa, sai dai kuma lamarin ya canja a wajen daurin auren bayan amaryar ta gano cewa angon da za ta aura ba ma’aikacin banki bane, hasalima shi direban motar haya ne.
Matar mai suna Jackeline Wanjiru ta fito daga cikin cocin da ake daurin auren su ta Mbeeni a lokacin da taji cewa angonta mai suna Alfred Musa, wanda suka shafe shekaru 4 suna soyayya direban motar haya ne, ba kamar yadda ya sanar da ita cewa shi ma’aikacin bankin KCB ba ne.
Rahotannin sun bayyana cewa auren wanda aka yi yunkurin daurawa a ranar Laraba, an dakatar dashi bayan jin wannan abin kunya da ya faru.
Duk kokarin da abokanan ango da ‘yan uwa da abokanan arziki suka yi na ganin sun lallasheta ta koma an daura auren yaki yiwuwa.
To babban darasi dangane da wannan lamari dai shine, mu yi kokari mu zama masu fadar gaskiya a duk inda muka tsinci kan mu. Ku sanar da masoyanku ainahin irin aikin da kuke yi domin su so ku saboda yadda kuke ba wai saboda kudin ku ba.
Toh Allah Ya Kyauta Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Labari Mai Baj Dariya Da Mamaki.
Sannan Munaso Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe.
Ku Karanta Wannan:
Ku Karanta wannan:
Tsananin Kyau Na Ya Sanya Maza Ke Guduna Har Yanzu Bani Da Saurayi Cewar Hauwa
Ku Karanta Wannan: