Wasu Mutane Da ‘Yan Bindiga Da Ke Shirin Sacewa A Jihar Kaduna ‘Yansandan Jihar Sunyi Nasar Kamasu.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta yi nasarar wargaza yunkurin waɗansu ‘yan bindiga na sace wadansu mutane a Zaria.

‘Yan sandan sun kashe ɗaya daga cikin ƴan bindigar tare da kama wasu a unguwar Nagoyi da ke birnin Zazzau, a daidai lokacin da ‘yan bindigar suke kokarin satar mutanen gida.

Rahotanni na cewa ‘yan sandan sun yi nasarar ritsawa da `yan bindigan, har suka yi artabu da su, inda suka yi sa’ar kashe daya daga cikin ‘yan bindigar, yayin da ragowar suka ranta a na kare.

‘Yan sandan kamar yadda kakakin rundunar Muhammad Jalige ke cewa wani da suke zargin cewa gawurtaccen mai satar mutane ne ya fada komarsu.

Jihar Kaduna da sauran takwarorinta da ke shiyyar arewa maso yamma da kuma makwabciyarta, jihar Niger, duka suna fama da matsalar tsaro.

Kuma halin da ake ciki jami’an tsaro kama daga sojoji da ‘yan sanda da kuma ‘yan banga ko ‘yan sa-kai sun dukufa wajen daƙile wannan aika-aikar a yankin.

Ko a taron da kungiyar gwamnonin jihohin arewa da kuma sarakunan lardin suka yi, sai da suka yaba da kokarin da jami’an tsaron ke yi, har ma suka bukaci a rinka daukar mataki na bai daya a yankin ta yadda za a yi wa ‘yan bindigar rufin-ganga.

To jama’a zaku iya ajiyemana ra ayoyinku a sahinmu na tsokaci Domin Jin tabakin ku akan wannan kada ku manta Kuna tare dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews.

KU KARANTA WANNAN:

Jarumi Musa maisana’a ya bayyana Dalilin da yasa ba’a ganinsa fim da kuma dalilin da yasa ake kiransa da Musa maisana’a

Tofa Wata Sabuwa Ana Wata Ga Wata Ali Nuhu Yayi Amai Ya Lafai Kan Maganar Da Yayi A Baya

Sanda Episode 1 || season 1 With English Subtitle 2021

Maganar Auren Hadiza Gabon Da Malam Isah Ali Pantami Karyane Amma Rigima Ta Barke Akan Haka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button