Yadda Na Koma Bara A Bakin Titi Bayan Korata Da Akayi Daga Aikin Banki

Wannan Labarin Zai Baka Darasi Mai Yawa Akan Wannan Bawan Allahn Domin Kuwa Idan Ka Tsaya Ka Karanta Labarinsa Zaka San Ya Tafka Asara Babba, Sannam Kuma Kaima Mai Karatu Zaka Dauki Darasi Saboda Gudun Shiga irin Rayuwar Daya Fada.
Wannan Wani Tsoho Ne Wanda Ake Kira Da mwangi Wanda Asalin Aikinsa Shine Manajan Banki Kuma Yana Samun Kudi Sosai Domin Shine Babban Manajan Banki Na Kasar Kenya.
Kamar Yadda Muka Samo Labarinsa A Shafin Labaran Hausa Daga Facebook, Labarin Nasa Ya Fara Kamae Haka;
Wannan shine abinda ya faru da Ben Mwangi, wanda labarin shi ana iya haska shi a cikin fim saboda yadda rayuwa tayi da shi. Ben Mwangi ya samu nasarar zama manajan banki a shekarar 1970, indaa ya tara dukiya mai yawan gaske, sai dai yadda ya dauki rayuwa ya sanya a karshe ya kare yana bara a titi na tsawon shekaru 15.
Mwangi wanda yanzu yake da shekaru 76 a duniya, akwai lokacin da ya zama yana daya daga cikin makusanta na manyan kasar Kenya, ciki kuwa hadda daya daga cikin wadanda suka samar da kasar Kenya, kuma tsohon shugaban kasar Kenya, wato Mzee Jomo Kenyatta.
Mwangi ya fara haduwa da Kenyatta a wajen wani taro da abokin shi ya hada a ranar 30 ga watan Disambar shekarar 1968, shekaru biyar kacal bayan kasar Kenya ta samu ‘yancin kai.
A wajen taron ne shugaban kasar ya rubuta takarda zuwa ga wani bankin kasuwanci dake a birnin Nairobi akan a bawa Mwangi aiki.
Wannan takarda ta sanya ya samu nasarar zama manajan banki na tsawon shekara takwas, damar da ya bata daga baya kenan.
A shekarar 1976, an kori Mwangi daga aiki, bayan zargin shi da aka yi da satar kudi. Wannan dalili ne ya sanya shi neman taimako daga wajen Kenneth Stanley Njindo Matiba, wanda a lokacin makwabcin shi ne a kauyen su dake Kiharu.
Ba tare da nuna gajiyawa ba a kokarin da yake, Mwangi yakan kaiwa Matiba ziyara, wandaa a lokacin babban dan siyasa ne. Matiba ya yiwa Mwangi alkawarin bashi aiki cikin mako daya, inda kuma ya cika wannan alkawari, ya dauke shi a matsayin akawunsa.
Sai dai an ce mai hali baya fasa halinsa, domin kuwa Mwangi ya tafkawa Matiba uwar sata, inda da bakin shi a wata hira da aka yi da shi a ranar 21 ga watan Satumbar shekarar 2021 da jaridar The Standard, ya ce:
Hatta Shi Kanshi Matiba Din Sai Danayi Masa Satar Kudi A Shekara Ta 1978.
Matiba Ya Mareni, Ni Kuma Alokacin Na dakeshi Acikinsa, Sai Akazo Aka Rabamu Daga Nan Ya Koreni.
Matiba daga baya ya kori Mwangi dagaa aiki, wanda daga baya ya zama dan damfara, inda ya dinga damfarar bankuna na tsawon shekara biyar.
Wannan ya yi sanadiyyar kama shi da abokanan aikin shi, inda suka shafe shekaru uku a gidan yari. Bayan an sake su lokacin yana da dan sauran kudi a ajiye, Mwangi ya fada rayuwa ta almubazzaranci, inda yake kashewa mata kudi da shaye-shaye.
Wannan rayuwa da ya dauka ta sanya daga baya, babbar akawun ya fada cikin matsanancin talauci, daga baya ya fara aikin karfi don ya samu abinda zai yi rayuwa. Wannan lamari ya sanya Mwangi ya koma kwana a titi saboda ko gida bashi da shi.
Ina da kudi sosai a lokacin da nake manajan banki, da kuma lokacin da nake aiki karkashin Matiba, sai dai duka wannan kudaden na kashe su a banza na bawa mata sauran kuma nayi shaye-shaye, ya ce.
Zamu so Mu Karbi Ra’yoyinku Akan Wannan Mummunan Halaye Nasa A Shashenmu Ma Comment Sannan Munaso Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.
Ku Karanta Wannan:
Ku Karanta Wannan:
Ku Karanta Wannan:
Yadda Amarya Ta Gudu Lokacin Daurin Aure Bayan Ta Gano Mijin Dazata Aura Direban Motar Haya Ne