Jami’an ‘Yansandan Abuja Sun Watsawa ‘Yan shi’a Barkono Tsohuwa Yayin Tattaki A Abuja.

Kungiyar harka Islamiyya ta ‘yan shi’a a Najeriya ta yi zargin cewa an kashe mabiyanta lokacin da ‘yan sanda suka tarwatsa jerin gwanon tattakin da suke yi na ranar arba’in a ranar Talata a Abuja.

Haka kuma kungiyar ta ce an jikkata mabiyanta da dama sannan wasu da yawa ba a san inda suke ba.

Sai dai ‘yan sanda sun ce babu wanda ya rasa ransa a hargitsin.

Daruruwan mabiya shi’a ta harka Islamiyyar sun yi zargin cewa ‘yan sanda sun auka musu a yayin da suke gudanar da tattakin arba’in don tuna wa da halin da jikan Manzon Allah Imam Hussain ya shiga a karni na bakwai a Karbala, wanda a cewarsu duk shekara suna yi.

Sun bayyana haka ne lokacin da suka kira wani taron manema labaranmu na Dalatopnews dake  Abuja sun bayan faruwar lamarin.

Sakataren dandalin harka Islamiyya mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky Malam Abdullahi Muhammad Musa ya shaida wa Dalatopnews cewa, suna kan hanyar shiga cikin Abuja a dai-dai Gwarimpa, sai suka ji an jefa musu barkonon tsohuwa.

Bugu-da-kari Abdullahi ya ce akwai wadanda ba a gansu ba, inda suke kan tattara yawan wadanda suka batan, ciki har da wadanda ba su ji ba su gani ba.

Sannan ya ce fiye da mutum goma sha daya sun jikkata yayin tattakin.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin Abuja Josephine Adeh, ta ce ba haka lamarin yake ba, hasalima mabiya shi’a ne suka far musu, amma ta ce sun kama wasu daga cikinsu da dama dauke da makamai.

‘Yan kungiyar dai sun sha yin artabu da jami’an tsaro a  ‘yan shekarun nan a Najeriya.

To jama’a zamu so mu larbi ra’ayoyinku akan aukuwar wannan lamarin a sahinmu na tsokaci.

Kada kumanta kuna tare dani A.Usman Ahmad dauke da labaran Duniya.

KU KARANTA WANNAN:

Wasu Mutane Da ‘Yan Bindiga Da Ke Shirin Sacewa A Jihar Kaduna ‘Yansandan Jihar Sunyi Nasar Kamasu.

‘Yan fim ba malamai bane sai dai muna fadakarwa ga al’umma, cewar jarumi Falalu a Dorayi

Jarumi Musa maisana’a ya bayyana Dalilin da yasa ba’a ganinsa fim da kuma dalilin da yasa ake kiransa da Musa maisana’a

Sanda Episode 1 || season 1 With English Subtitle 2021

Maganar Auren Hadiza Gabon Da Malam Isah Ali Pantami Karyane Amma Rigima Ta Barke Akan Haka

Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button