Yakamata ‘yan Nigeria Su Godewa shugaban kasa Muhammad Buhari inji KungiyarKare Hakkin Musulmai Ta MURIC ?

Kungiyar Kare Hakkin Musulmai ta MURIC ta ce talura da yadda matsalar man fetur ke tsamari a Burtaniya ya kamata ‘yan Najeriya su gode wa Shugaba Muhammadu Buhari.

A yammacin yaune muka tsinci wani labari Wanda kungiyar Kare hakkin musulma ta MURIC ta ce ‘yan Nigeria su godewa baba Buhari a kasar.

Wanda rahotan yake cewa a sanarwar da MURIC ta fitar, daraktan kungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya ce a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari ba a rika fuskantar dogayen layuka a gidajen mai ba.

Kusan makonni biyu kenan ana samun dogayen layuka a gidajen mai a Burtaniya.

Kuma rahotanni sun nuna cewa gidajen mai 5,500 daga cikin 8,000 ba su da man kwata-kwata.

Lamarin ya sa Firanminista Boris Johnson ya ce gwamnatinsa za ta ba da biza ga dirabobin tankokin mai 5,000 daga kasashen waje don su yi aikin dakon mai a kasar.

A cewar Farfesa Akintola “karancin man fetur a Burtaniya ya haifar da karancin abinci da turmutsitsi a gidajen mai.

“Bugu da kari yanzu haka gwamnati na duba yiyuwar rufe makarantu.”

Ya kara da cewa “hakan ya nuna cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta yi namijin kokari wurin magance matsalar karancin man fetur da ta zame wa gwamnatocin baya matsala,” in ji Farfesa Akintola.

Kada Kumanta Kuna tare Dani A.Usman Ahmad A shafinmu na Dalatopnews Dauke da Labaran Duniya.

KU KARANTA WANNAN:

Tirkashi Ashe Ado Gwanja Da Adam A Zango Sun Kashe Mutum 4 A Kasar Niger

Sojojin Nigeria Sun Kashe Masunta Sama Da 18 A Jiahar Barno.

Rahama sadau ta sake wallafa wasu hotunanta tare da dan india a wajan daukar fim wanda suka janyo cece-kuce

Kucigaba da kasancewa tare damu a shafinmu na Dalatopnews kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button