An Daina Yin Achaba A Jihar Kaduna Daga Yanzu

Kamar Yadda Shafin premium Times Ya Rawaito Sun Bayyana Yadda Hukumar Tsaro Ta Jihar Ta Dakatar Da Yan Kabukabun Achaba Domin Gudanar Da Tsaro.

Acikin Bayaninsu Wanda Ya Fara Kamar Haka Gwamnatin Kaduna Ta Sanar Da Dakatar Da Kabukabun Achaba A Jihar, Har Sai Lokacin Da Allah Yayi Babu Ranar Da Ake Zaton Barinsu Su Ci Gaba Da Fita Aiki.

Hakan Da Kuma Wasu Dokoki Na Kunshe Acikin Wani Jawabi Da Kwamishinan Tsaro Ma Jihar Yayi A Ranar Laraba.

A Cikin Jawabi Samuel Aruwan Ya Bayyan Wani Wasu Matakai Da Gwamnatin Ta Dauka Ga Dan Achaban Daya Karya Doka Kamar Haka:

Duk Wanda Aka Kama Da Yin Aikin Achaba Za’i Dandana Kudarsa.

An Hana Keke Napeep Zasu Fara Aiki Daga 7 Na Safe Zuwa Karfe 6 Na Yamma, Idan Kuma Ka wuce Haka Duk Abunda Yafaru Akanka Kai Ka Janyo. 

Duk Wata Motar Haya A Kaduna dole Tayi Fentin Ruwan Kwai Da Baki, Haka Ma Tasi-Tasi Wannan Kalar Fentin Zasuyi.  

Babu siyar da mai a jarkoki a kananan hukumomin Birnin Gwari, Kauru, Kachia, Kajuru, Chikun Giwa, Igabi, Kagarko. 

An hana safarar itace da gawayin girki a motoci, shiga ce ko fita.

An dakatar da cin kasuwannin mako-mako a kananan hukumomin Igabi, Birnin Gwari, Giwa, Kajuru da babbar kasuwar mako-mako da ake ci duk Talata ta Kawo. 

Gwamnati ta ce an ɗauki wannan makati ne domin a jama’a ba don son rai ba.

Wasu mutane ƙalilan sun jefa mutane da yawa cikin halin ƙaƙanikayi babu gaira babu dalili. Ba za a bari hakan ya ci gaba ba, dole a bi duk hanyar da za abi a kawo harshen.

Wannan Shine Abunda Aka Bayyana A Sabbi  Dokokin Da Aka Fitar A Jihar Kaduna Game Da Yan Achaba.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Ma Tsokaci Akan Wannan Sabon Al’amari Daya Faru A Jihat Kaduna Wanda Zai Iya Kawo Rashin Aiki Ga Mutane Da Dama A Jihar.

Toh Allah Ya Kyauta Munaso Ku Watsa Labarin Nan Domin Yaje kunnen Mutand Dayawa Daga Cikin Jihar Kaduna Domin Su Saj Halin Da Ake Ciki.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Zamu Tsayar Da Layukan Sadarwa A Jihar Kaduna Cewar Gwamna Nasiru El-Rufa’i

Ku Karanta Wannan Labarin:

Mutane 51 Suka Rasa Rayukansu A Yanking Kaduna A ‘Yan kwanakinnan Wanda Gwamnan Kaduna malam L Rufa’i

Ku Karanta Wannan Labarin:

Jami’an ‘Yansandan Abuja Sun Watsawa ‘Yan shi’a Barkono Tsohuwa Yayin Tattaki A Abuja.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button