Asirin Wani Mawaki Ya Tonu Mai Yin Lalata Da Kananan Yam Mata Ta Hanyar Yaudararsu Su Zama Taurari Kamarshi A Amurka R. Kelly

Asirin Wani Rikakken Manemin Mata Ya Tonu Mai Suna R. kelly Mawakine A Kasar Amurka Wanda Ya Kasance Ya Samu Daukaka Mai Yawa A Sana’arsa Ta Waka.
To Sai Dai Kuma Wani Abun Takaichi A Rayuwar Mawakin Shine A Yanzu Gwamnati Ta Kamashi Biyo Bayan Kamashi Da Akayi Da Laifin Yin Lalata Da Kananan Yam Mata Da Kuma Cin Zarafin Mutane.
R. Kelly Ya Dauki Tsawon Shekaru Yana Lalata Da Yara Kanana Wato Yam Mata Ta Hanyar Amfani Da Daukakarsa Wajen Matan Dasuke Zuwa Wajensa Domin Ya Koya Musu Waka.
Kamar Yadda Wata Majiya Ta Sanar An Kamashi Da Laifin Safarar Mata Zuwa Ga Wasu Kasashen Domin Yin Wannan Harka Ta Fasikanchi Dasu.
Yadda Asirinsa Ya Tonu Aka Garkameshi A Kurkuku Sannan Aka Tuhumeshi Da Karya Dokar Kasa Ta Bangaren Lalata Da Yara Kanana Mata Wanda Hakan Zai iya Yin Sanadiyyar Zamansa A Kurkuku Zuwa Karshen Rayuwarsa.
Kelly, wanda cikakken sunansa Robert Sylvester Kelly, an same shi da amfani da ɗaukakansa da arziki wajen yaudarar mutane ta hanyar alkawarta musu samun dama haskawa a bidiyon wakokinsa.
Da dama sun ce suna da karancin shekaru lokacin da aka yi lalata da su.
Kelly ya musanta duk wadannan zarge-zarge da aka gabatar a kansa.
Mawakin ya yi suna sosai a shekarun 1990 da wakarsa ta “Bump and Grind” da “Ignition”. Sannan wakarsa da ta yi fice a duniya ya yi ta ne a 2004 “I Believe I Can Fly”.
A lokacin da yake bada tarihinsa, R Kelly ya shaida cewa shi da kansa ya taba fuskantar cin zarafin lalata.
An kuma samu Kelly da karya dokar da ta haramta fataucin mata domin lalata a fadin Amurka.
An kuma sami shi da jogorantar gungun masu aikata irin wannan laifi, laifin da aka fi samu manyan kungiyoyin masu aikata manyan laifuka.
Amma a wannan shari’a alkalai sun same shi da jagorantar lalata da mata da yara domin bukatun kansa.
A lokacin shari’ar, masu gabatar da kara sun shaida yada manajojinsa, jami’an tsaro da sauran mukarabansa suka rinka taimaka masa wajen aikata manyan laifuka.
Alkalan sun kuma saurari yadda Kelly ya samu wasu kundayen bayanai ta haramtattun hanyoyi domin auren mawakiya Aaliyah lokacin da take da shekara 15. Ta mutu sakamakon hadarin jirgi a watan Agustan 2001.
Zamu So Mu Karbi Ra’yoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Badakalar Da Mawakinnan Yayi.
Munaso Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbi Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Ku Karanta Wannan Labarin:
Sojojin Nigeria Sun Kashe Masunta Sama Da 18 A Jiahar Barno.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Jami’an ‘Yansandan Abuja Sun Watsawa ‘Yan shi’a Barkono Tsohuwa Yayin Tattaki A Abuja.