Advertisement

Kotu Ta Yankewa Karuwar Da Ta ciji kwastomanta A Harshe Akan Yanemi?

Wata babbar Kotu a Makurdi a ranar Alhamis ta yanke hukuncin daurin wata hudu ga wata karuwa, Dooshima Anems, saboda cizon harshen kwastomanta yayin jima’i.

‘Yan sanda sun tuhumi Anems da harar kwastomanta da kuma haddasa mummunan rauni a harshensa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mai shari’a a kotun, Ms Rose Iyorshe, ta yankewa Anems hukunci bayan ta amsa laifin ta sannan ta shaidawa kotu cewa ta ciji Mista Amos Igbo ne don kare kanta. 

Iyorshe a cikin hukuncinta ta ba Anems zabin tsaftace harabar kotun na mako guda. 

Tun da farko, mai gabatar da kara na ‘yan sanda, Insp Veronica Shaagee ta shaida wa kotun cewa an cafke karuwar ne a ranar 28 ga watan Satumba.

Shaagee ta ce Anems ta ciji Mista Amos Igbo a harshen yayin jima’i a otal din Tekdee inda suka kwana.

Ta ce Igbo ya dauko Anems ne a Yaman Park ya kuma biya ta N2,000 a daren. 

Ta ce laifin ya ci karo da sashi na 166 (b) da 248 na dokokin Penal Code Cap 124 (2004) na jihar Benue.

Tun da farko, Anems ta bayyana cewa Igbo na son karin lokaci da ita sabanin kudin da ya biya amma ta ki.  

To wannan Sai dai muce Allah yakiyaye sannan zamuso muji ra’ayoyinku akan wanna batun zaku iya ajiyemana ra ayoyinaku a sahinmu na tsokaci da kulawa 

KU KARANTA WANNAN:

Bazan Taba Fitowa A Fina-Finan kudu ko Wata Kasar Ba Inji Jarumar Masana An Tar Kannywood Umma Shehu Saboda Akwai.

Kada kumanta ku Danna Mana alamar kararrawar sanarwa.

Innalillahi: Gaskiyar labari kan mutuwar jarumin kannywood Dadi wanda kuka fi sani da Abale

Saban cece-kuce ya farke kan sabuwar wayar da Ummi Rahab ta saya iphone 13 pro max wanda kudinta yakai kimanin Naira 930k

 

Kuci gaba da kasancewa tare Dani A. Usman Ahmad A shafinmu na Dalatopnews Domin samin labarn Duniya Baki Daya.

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button