Maharan Sun kuma Cinna Wa Rumbuna Hatsi Wuta Tare Da Sace Mata Da kayan Abinci Masu Dumbin Yawa.

Rahotannni daga jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya na cewa a kalla mutum ashirin ne suka mutu kana wasu da dama suka jikkata sakamakon wani hari da ‘yan bindiga suka kai garin Gatawa cikin karamar hukumar Sabon Birni.

Shaidu sun ce maharan sun kuma cinna wa rumbuna hatsi wuta tare da sace kayan abinci masu dumbin yawa.

Wannan harin dai na zuwa sa’o’i ashirin da hudu da ‘yan bindigar suka aukawa garin Gangara mai makwaftaka.

Wadanda suka shaida harin sun bayyana wa BBC cewa ‘yan bindigar sun auka wa garin Gatawa ne ranar Talata da marece inda suka ci karensu babu babbaka har zuwa wayewar gari.

Wani matashi da aka sace wa yar uwa, ya ce maharan sun yi harbe-harben kan mai uwa da wabi, abin da ya sa mutane suka yi ta-kai-ta-kai.

Sannan ya ce sun kona dammunan hatsi masu dumbin yawa. Mutumin ya kara da cewa akasarin al’ummar garin sun tsere. Sai dai ya ce ba su san adadin wadanda suka mutu ba, kasancewar mutane sun tarwatse don tsira da rayukansu.

“Duk ga mu nan mun yi gudun hijira, mazanmu da mata da yara.

Wasu sun gudu Nijar wasu sun tafi garuruwa da ke makwabtaka. Wasu sun samu guduwa da dabbobinsu.

“An tafi da kanwar babana, garin ya yamutse, abinbci ma ba mu da shi.”

Ita ma wata matar da ta tsallake da kyar zuwa Sokoto ta shaida min ta waya cewa ‘yan bindigar sun tafi da diyarta.

“Mu mata muan cikin gida sai dai idan mun ji harbe-harbe muke samun guduwa. Muna cikin gida kawai sai ga su sun shigo gida, muka samu muka tsere, amma cikin wadanda suka kwasa har da ‘ya’yana,” in ji ta.

Kuna sauraran labaran Duniya kaitsaye daga shafinmu na Dalatopnews.

KU KARANTA WANNAN:

Asirin Wani Mawaki Ya Tonu Mai Yin Lalata Da Kananan Yam Mata Ta Hanyar Yaudararsu Su Zama Taurari Kamarshi A Amurka R. Kelly

Yakamata ‘yan Nigeria Su Godewa shugaban kasa Muhammad Buhari inji KungiyarKare Hakkin Musulmai Ta MURIC ?

Tirkashi Ashe Ado Gwanja Da Adam A Zango Sun Kashe Mutum 4 A Kasar Niger

innalillahi Kalli Rayuwar Hamza Yahaya Jarumin Kannywood Bayan Rashin Lafiyarsa

Sojojin Nigeria Sun Kashe Masunta Sama Da 18 A Jiahar Barno.

Kuna tare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button