Sabuwar rigima a kannywood: Jaruman kannywood zasuyi sulhu tsakanin mawaki Nura M Inuwa da Abdul Amart mai kwashewa

Kamar yadda wasunku suka sani an sami ‘yar hatsaniya tsakanin mawaki Nura M inuwa da kuma Abdul Amart mai kwashewa.
Sai kuma a yanzu wani jarumi a masana’antar kannywood mai suna Aminu a Dagash ya wallafa wani rubutu wanda yake nuna rashin jin dadin sa kan wannan abin da yake faruwa tsakanin Mawaki Nura m Inuwa da kuma Abdul Amart mai kwashewa.
Inda yake kira ga manyan masana’antar kannywood da su gudanar da sulhu a tsakanin abokanan junan.
Karanta wannan labarin
Tirkashi Ashe Ado Gwanja Da Adam A Zango Sun Kashe Mutum 4 A Kasar Niger
Ya yau kuma muka sami labari daga shafin Hausaloaded kamar yadda shima ya sami labarin daga shafukan jaruman, inda wasu jama’a sukayi addu’ da yabo kan jaruman suna cewa sune abokai na arziki domin sunyi kira da agudanar da sulhu, wanda dama addinin musulinci yana bukatar idan an sami sabani to a sulhunta.
Ga dai abin da jaruman suka wallafa a shafukansu na sada zumunta kan wannan ‘yar hatsaniya dake faruwa tsakanin mawaki Nura m inuwa da Abdul Amart mai kwashewa.
Suke cewa gaskiya ya kamata magabata su shiga cikin maganar nan kamar yadda aka saba ako wace rashin fashimta a kannywood.
Karanta wannan labarin
Suka kara da cewa: Amintattun mutane biyu da duniya ta gamsu da nagartar amincinsu, Abdul Amart mai kwashewa da Nura m inuwa, ba zamu bari din kakkiyar kwarya ta fashe ba, kuma ace ta gagari dinki ba.
Wannan shine abin da suka wallafa a shafukan su na sada zumunta instagram, domin a sami sulhu tsakanin mawaki Nura m inuwa da Abdul Amart mai kwashewa.
Karanta wannan labarin
innalillahi Kalli Rayuwar Hamza Yahaya Jarumin Kannywood Bayan Rashin Lafiyarsa