Tirkashi Kotu Ta Hana Bayar Da Belin Abduljabbar

Babbar Kotun Addinin Musulunchi Dake Kofar Kudu Karkashin Ustaz Ibrahim Sarki Yola Tayi Watsi Da Neman Belin Da Lauyoyin Sheik Abdulajabbar Sukayi.
Kamar Yadda Gidan Jarida Na Freedomradionig Ya Rawaito Game Da Abduljabbar Sun Wallafa Wannan Labarin Game Fa Hana Belin Malam Abduljabbar.
A Zaman Kotu Na Ranar Alhamis, lauyoyin Gwamnati Sun Gabatar Da Kansu Karkashi Barisata Mamman Lawan Yusufari SAN Na Kotun.
Baya Da Haka Lauyoyin Malamin Sun Bukaci Kotu Data Bayar Da Kwafin Takardar Shari’ar A Baya, Domin Wannan Shine Karonsu Na Farko A Bayyana A Gaban Kotun, Sannan Sun Bukaci Maus Kara Su Gabatar Da Shaidunsu.
Sannan Kotun Ta Waiwayi Lauyoyin Gwamnatin Da Suka Ce Basu Suka Bayar Da Kwafin Shari’ar Ba.
Baya Da Haka Game Da Gabatar Da Shaidu Lauyoyin Gwamnati Sunce A Shirye Suke.
Kotun Ta Bayyana cewa, Tuni Aka Aika Da Kwafin Shari’ar Sai Dai Lauyoyin Abduljabbar Sunce Basu Aka Bawa Ba.
Sannan Lauyan Malamin Ya Nemi Da Abashi Belin Malamin, Sai Dai Lauyoyin Gwamnati Sunyo Suka Akan Lamarin.
Daga Karshe Kotun Taki Amincewa Da Bayar Da Belin Malamin.
Sannan Mai Shari’a Sarki Yola Ya Dage Karar Zuwa 14 Ga Watan Oktoba A Shekara Ta 2021.
Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku Akan Wannan Shari’a Ta Malamin Addini Wato Sheik Abduljabbar Da Gwamnatin Kano.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Ku Karanta Wannan Labarin:
Zamu Tsayar Da Layukan Sadarwa A Jihar Kaduna Cewar Gwamna Nasiru El-Rufa’i
Ku Karanta Wannan Labarin:
Jami’an ‘Yansandan Abuja Sun Watsawa ‘Yan shi’a Barkono Tsohuwa Yayin Tattaki A Abuja.