Akwai Babbar Cutarwa Akan Auren Kananan Yam Mata Da Tsofaffin Maza Sukeyi Yanzu

Kamar Yadda Kuka Sani A Yanzu Ana Tsaka Dayin Wani Abu Wanda Ake Masa Lakabi Da Kalmar Wuff Yadda Zakaga Tsofaffin Mutane Suna Auren Yam Mata Kanana Masu Karanchin Shekaru.
A Wani Dogon Bayani Da Muka Samu Daga Shafin Facebook Na Wani Mutumi Ya Bayyana Cewa Akwai Babbar Cutarwa A Wannan Auren Kamar Yadda Bayaninsa Ya Fara Kamar Haka;
AKWAI BABBAR CUTARWA A CIKINAUREN KANANAN YAN MATA DA WASUMAZAN MASU YAWAN SHEKARU SUKEYI.
Addininmu bai haramta namij! meshekaru da yawa ya auri karamar yarinya
ba, amman kuma ya haramta namiji ya
auri macen da bazai iya sauke mata
dukkan nauyinta dake kansa ba,Wajibinka ne ka sauke dukkan hakkin
matarka dake kanka, kamaa tun daga ci
da shanta, sutura, lafiya, muhalli,
Walwala har zuwa kan shimfida.
Dukkanhakkinta guda daya da ka gaza saukeshi,
to Allah zai tuhumeka akan wannan hakkida ka tauye mata.
Ta wurare da dama manyan mazaje
masu yawan shekaru suna tauye hakkin
matansu kanana, idan sukayi magana sai
suce ai yanzu girma ya kamasu, bai
kamata a gansu suna aikata kaza, ko
kuma suna sanya sutura iri kaza ba,
kasan da hakan amman kaje ka dakko
karamar yarinya wadda dole tana bukatar
wadannan abubuwan?Dalilina na yin wannan rubutun…
Wani babban mutum ya sameni akasuwa da vake tamu taz70 dava dashi Wani babban mutum ya sameni a
kasuwa, da yake tamu tazo daya dashi
sOsa, yake cemin yana cikin damuwa
sosai, nace dashi me yake damunka?
Yace dani matarsa, nace kamar yaya
matarka? Yace dani eh ita, amman
amaryar wadda ya auro watanni 5 da
suka gabata, cikin kulawa sosai nace
dashi bata da lafiya ne?Yace dani ai har gara rashin lafiya, da
mamaki sosai na kalleshi ina mai cewawannan kam wanne irin abune wandahar gara rashin lafiya dashi?Yace dani wallahi tana damunsa ne akanlallai sai ya canza wasu daga cikin
dabiunsa da kuma kalar suturar da yakee
sanyawa.
Kullum kiranta a garesa shine
ya fara tara gashi, sannan ya dinga yiwa
kansa dayiss saboda farin gashin dake
kansa ya boye, tana mai cewa dashi
tanason taga gashi sosai a kansa ta
yanda zata dinga sanya hannunta akansa
taji dumuss din gashin.
A bangaren sutura manyan kayan da
yake sanyawa sun isa haka, tana
kwadaita masa cewa yaje kasuwa ya
sayo irin wandunan nan wadanda suke a
yage daga Gwuiwa, sannan ya sayo
kananan riguna, duk zasu dinga yi masa
kyau sosai, kuma ita tafi son ganinshi ahaka.Bata damuwa da yawan yayan da yake
dasu, a gabansu sai ta dinga kiransa da
suna Baby, idan kuma yaki amsawa ranta
ya baci, akwai lokacin da tace dole sai ta
bashi abinci a baki, amman yaki yarda,
ganin ranta ya baci sosai ya amince zai
karba, ta fara bashi kenan, sai ihun yara
sukaji suna cewa ana baiwa baba abinci
a baki.
Daidai da wayarsa sai da ta dauka ta
canza sunanta akan numberta, ta sanya
suna irin na masoyan zamanin nan,
alhalin sauran matansa guda biyu
Suwaiba da Maman yara ya sanya.
Dadaisauran abubuwa da yawa da yayi ta
zayyanomin wadanda ni a fahimtata
kacokam shine da laifi.
Tayaya kana dan shekara 50+ zakaje ka
auro macen da take da shekara 18-22,
alhalin kuma baka tsarawa kanka sakkoda rayuwarka zuwa daidai da shekarunta
ba?Karamar mace tana bukatar a nuna matasoyayya agaban koma waye, koda kuwa
a gaban iyayenta ne, tana bukatar kuyi
wasa tare, kuci abinci tare, kuyi wanka
tare, kuyi wasannin gudu har maa da
tsere, tana bukatar ka jefata sama tadawo kasa ka cabe kayarka, tana bukatar
cakulkulu a wasu lokutan, duk wani
nau’in wasa ko kuma abinda yayi daidai
da zamaninta tana bukatarsa,A wasu lokutan tana bukatar ka fitayawon shakatawa tare da ita, duk maa ba
wannan ba, wallahi akwai lokacin dabukatarta shine tayi maka waka ko kuma
ta kunna maka, kai kuma ka tashi ka tikarawa a gabanta, duk kasan baka shirya
yin wadannan ba kaje ka aurota?
Wannan cutarwa ce mafi muni, domin ka
tauye mata hakkinta me yawa, da ka
barta ta auri me daidai da shekarunta,
watakila da hakan bata kasance ba.
Amatsayinka na babban mutum, idan
har kasan baka shirya sakko da
rayuwarka zuwa daidai da na karamar
mace ba, don Allah kada ka aureta,domin akwai zunubai masu tarin yawa a
Cikin tauye hakkin matar da ka aura, kaje
ka nemo bazawara ko kuma waddashekarunta itama suka ja, ita zata
amsheka a duk yanda ta sameka.
Allah yasa mu dace.